Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a babban birnin Najeriya wato Abuja, ta yi watsi da karar da jam’iyya mai mulki a kasar ta APC ta shigar wadda ta zargi Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo da gabatar da shaidar karatu ta boge.
Alkalin da ya jagoranci zaman kotun a ranar Asabar, Mai Shari’a Ahmed Mohammed ne ya yi fatali da karar wadda jam’iyyar APC ta shigar tare da wani jigo na jam’iyyar mai suna Williams Edobor.
- Masu garkuwa da mutane sun sace Yara 6 ’yan gida daya a Zamfara
- Ganduje zai ba Kwankwaso sarautar mahaifinsa
- Ko Arewa24 sun nemi in dawo Kwana Casa’in ba zan dawo ba –Safara’u
Yayin zartar da hukuncin nasa, Mai Shari’a Ahmed ya ce laifin da ake tuhumar gwamnan da shi babba ne, sai dai masu kararsa sun gaza gabatar da tabbatacciyar hujja a kan zargin da suke yi.
An zargi Obaseki da gabatarwa Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC takardun shaidar karatu na bogi yayin tsayawa takarar kujerarsa a wa’adi na biyu yayin zaben Gwamnan jiharsa da aka gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.
Obaseki ya yaba da hukuncin da Kotun ta zartar
Gwamna Obaseki ya bayyana hukuncin da Babbar Kotun Tarayyar dta zartar dangane da zargin da jam’iyyar APC take masa na gabatar da shaidar karatu na bogi a matsayin gagarumar nasara a kan tafarki na shari’a.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya ce hukuncin da kotun ta zartar wata shaida ce kan cewa komai rintsi sai gaskiya ta yi halinta duk yadda masu kin gaskiya suka shiga suka fita.
A cewarsa, “Hukuncin da Babbar Kotun ta zartar wanda Mai Shari’a Ahmed Mohammed ya gabatar, ’yar manuniya ce ta nuna fifikon da koda yaushe gaskiya take da shi a kan karya.”
“Babu nasara a yunkurin da wasu suka yi don ganin an murde fatan al’ummar Jihar Edo ta bayan fage kuma a yanzu muna cikin farin cikin ganin yadda gaskiya da ta yi halinta.”
Ya ce wannan hukunci da kotun ta zartar ya sake tabbatar da cewa mutanen Jihar Edo suna da kyakkyawar fahimta wajen nuna amincewarsu da shi a matsayin jagora da hakan ya kai ga sun jefa masu kuri’u a zaben gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar 19 ga watan Satumban bara.
Ya sha alwashin jajircewa wajen fifita ci gaban jihar fiye da komai ba tare da la’akari da masu neman huce haushin rashin nasarar da suka yi a zaben gwamnan jihar ba.
“Ina mika godiya ta musamman ga Hukumar Shari’a wacce ta tsaya tsayin daka don ganin gaskiya ta yi halinta, da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da Jam’iyyata ta PDP da kuma Shugabannin da Mambobin da magoya baya da al’ummar Jihar Edo da kuma daukacin ’yan Najeriya baki daya,” inji shi.