Kungiyar ‘Yan Jarida ta kasa reshen jihar Gombe (NUJ) ta rantsar da sababbin shugabanninta wadanda za su jagorance ta tsawon shekara uku.
A jawabinsa, sabon shugaban, Kwamared Sa’idu Bappah Malala, ya gode wa mambobin kungiyar kan hadin kai da suka ba shi, wajen sake zabar shi a karo na biyu.
- Matashi ya kone kansa saboda ya gaza biyan kudin jarrabawa
- Haramta kiwon-sake ba zai yiwu ba a wasu jihohin —Zulum
“Zan yi aiki da kundin tsarin mulkin kungiya na tabbatar da duk wasu kudaden kungiya an yi aiki da su ta hanyar da ya kamata ba tare da karkatar da su ba” inji Malala.
Ya ce zai jajirce wajen tabbatar da bin hakkokin mambobinsa don karfafa musu gwiwar gudanar da aikinsu.
Malala ya kuma ce zai yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ya sake ciyar da kungiyar gaba, sannan zai tsaya wajen ganin an kammala aikin sakatariyar NUJ da aikin gininta ya kai kimanin kashi 80 cikin 100.
Ya kara da cewa zai ci gaba da kokarin ganin ‘yan jarida a jihar suna samun horo kan ayyukansu musamman a bangaren fasahar zamani.
A nasa jawabin, Sakataren kungiyar na shiyyar Arewa Maso Gabas, Suleiman Baba Gimba, ya taya su murna sannan ya hore su da su zama jakadu na gari.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban Kungiyar Ma’aikatan Rediyo da Talabijin (RATTAWU) na jihar, Sani Abdullahi Gwani, cewa ya yi NUJ da RATTAWU Danjuma ne da Danjummai, tare suke aiki a kowanne waje.
Gwani ya kira su da su guji nuna bambancin addini ko na kabila a aikinsu, su hada kai su yi aiki tare su ciyar da kungiyoyin gaba.
Wadanda aka rantsar sun hada da Emmanuel Akila, Mataimakin Shugaba, da Danjuma Kala a matsayin Sakatare, da Sylvanus Alama Kalbore, Mataimakin Sakatare.
Sauran sun hada da Rabeca Caleb Maina, Mai Ajiyar Kudi, da Balkisu Bibi Lokuto, Sakatariyar Kudi, da Abubakar Sadiq Ahmed, Mai Binciken Kudi.