Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya yi rashin ɗan uwansa, Salihu Ahmadu Ribadu.
Salihu, wanda ba shi da lafiya, ya rasu ne a Yola, babban birnin Jihar Adamawa a ranar Lahadi.
- Babu dalibar firamare da aka lalata a Kano —Kwamishina
- Ruwan sama ya lalata gidaje 200 da makarantu a Filato
Domin jajantawa iyalan Ribadu, Shugaba Bola Tinubu ya aika da ayari na manyan jami’an gwamnati ƙarƙashin jagorancin Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa.
Da yake jawabi a gidan iyalan Ribadu da ke Yola, Gabajabiamila ya ce, Shugaba Tinubu ya yi alhinin rashin da aka yi wanda ya bayyana a matsayin mai raɗaɗi.
“Shugaban kasa ya umarce mu da mu zo Yola mu yi ta’aziyya tare ga daya daga cikin hadimansa mai kima, mai ba da shawara kan harkokin tsaro da kuma sauran ’yan uwa bisa wannan rashi da suka yi.
“Rashin dan uwa na kusa irin wannan abu ne mai matukar zafi, don haka yana da muhimmanci abokai da ’yan uwa su hadu wuri guda domin jajanta wa iyalan wadanda suka rasu,” in ji Honorabul Gbajabiamila.