Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.
Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.
Da yake jawabi gabanin miƙa su a hukumance, Shugaban Cibiyar NCTC, Manjo-Janar Adamu Laka, ya bayyana cewa jami’an tsaro daga sojoji, jami’an DSS, ’yan sanda da sauran hukumomin sun yi aiki ba dare ba rana domin ganin an ceto su.