✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NNPP ta yi watsi da sakamakon zaben Gwamnan Taraba

Ya ce ya tabbatar shi ya kashe zaben, kuma zai tafi kotu

Dan takarar jam’iyyar NNPP a Jihar Taraba, Farfesa Sani Muhammad Yahaya, ya yi watsi da sakamakon zaben Gwamnan Jihar wanda ya ba jam’iyyar PDP nasara.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Agbu Kefas na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar Asabar.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai a Jalingo, babban birnin Jihar ranar Talata, Farfesa Yahaya ya ce sakamakon da INEC ta bayyana sam bai yi daidai da wanda aka kada a rumfunan zabe ba.

Ya ce ya yi amannar shi ne ya lashe zaben amma aka murde shi ta karfin tuwo, inda ya sha alwashin bin hakkinsa ta kowacce hanya da doka ta tanada don kwato nasararsa.

“Nasara tamu ce, kowa a Taraba ya san mu muka lashe wannan zaben, saboda haka za mu bi matakin shari’a domin kwato hakkinmu,” in ji shi.

Daga nan sai dan takarar ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankali kada su dauki doka a hannunsu, zai bi mataki na shari’a.

A wani labarin kuma, dan takarar jam’iyyar APC a zaben, Emmanuel Bwacha, ya ce ya rungumi kaddara, kuma ya taya wanda ya lashe zaben murna.

Yanzu haka dai harkokin kasuwanci da zaman lafiya sun dawo garin na Jalingo, bayan wata arangama da aka samu tsakanin sojoji da ’yan sanda ranar Litinin.

Dan takarar na NNPP dai ya samu kuri’a sama da dubu 202 ne, inda ya zo na biyu a zabe, yayin da takwaransa na PDP ya lashe shi da kuri’a sama da dubu 255.