Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar NNPP na kasa a ranar Talata ta sanar da korar Kwamitin Amintattu na jam’iyyar na kasa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Kwamitin Amintattun jam’iyyar ya sanar da korar dan takararta na Shugaban Kasa a zaɓen da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso.
- Jam’iyyar NNPP ta dakatar da Kwankwaso daga cikinta
- ’Yan sanda sun kama sama da mutum 100 saboda auren jinsi daya a Delta
Sai dai Kwankwaso bai halarci taron ba.
Aminiya ta rawaito yadda kwamitin ya sanar da dakatar da Kwankwaso yayin taron ta a Legas, ta sanar da dakatar da Kwankwaso saboda zargin yi wa jam’iyyar zagon kasa.
Kazalika, kwamitin amintattun ya sanar da nada Dokta Agbo Major a matsayin mai rikon mukamin Shugaban jam’iyyar na kasa, sai Ogini Olaposi a matsayin Sakataren riko da wasu mutum 18.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar dakatarwar za ta yi aiki ne na tsawon wata shida.
Da yake yi wa ’yan jarida jawabi a karshen taron a Legas ranar Talata, Sakataren Kwamitin Aminitattun, Babayo Muhammad Abdullahi, ya zargi Kwankwaso da kulla alaka da Shugaban Kasa Bola Tinubu ba tare izininsu ba.
Kazalika, jam’iyyar ta ce tsohon dan takarar tata na alaka da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP.
Jam’iyyar ta kuma ce ta tube wa Kwankwason rawaninsa na Jagoran jam’iyyar na kasa.
Sakataren Kwamitin ya ce dakatarwar na da alaƙa da yi wa Kundin Tsarin Mulkin jam’iyyar karon tsaye.
To sai dai a yayin taron Kwamitin Zartarwar jam’iyyar da ya gudana a Abuja, NNPP ta ce ta kori masu taron na Legas saboda kokarin kawo mata. baraka.
Taron Kwamitin Zartarwar dai ya samu halartar Gwamnan Jihar Kano, wanda shi kadai jam’iyyar ke da shi, Abba Kabir Yusuf, da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Jibrin Falgore.
A cewar Shugaban jam’iyyar na Kasa, Alhaji Abba Kawu Ali, kwamitin nasu na kokarin farfaɗo da jam’iyyar ne daga rikicin da ta fada.
Ya kuma bukaci wadanda suka lashe zabe a tutar jam’iyyar da su yi koyi da Kwankwaso sannan su kasance jakadunta na gari.
Ya kuma ce sun yi taron ne domin su canza alamar jam’iyyar, wanda hakan ya ce na bukatar amincewar ’ya’yanta kafin a fitar da sabo.
A ’yan kwanakin nan dai NNPP ta sha fama da rikicin shugabanci inda Kwamitin Zartarwarta ya kori shugabannin jihohi bakwai da kuma wanda ya kafa ta a matakin kasa, Dokta Boniface Aniebonam da Sakatarenta na Yada Labarai na kasa, Dokta Agbo Major.