✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPC zai fara neman mai a kogunan Sakkwato da Benuwai

Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) zai juya akalarsa wajen nemo man fetur a Kogin Sakkwato da Mangagarar Kogin Benuwai bayan da ’yan Boko Haram…

Kamfanin Man Fetur na kasa (NNPC) zai juya akalarsa wajen nemo man fetur a Kogin Sakkwato da Mangagarar Kogin Benuwai bayan da ’yan Boko Haram suka kai harin da ya tilasta kamfanin dakatar da neman man fetur a tafkin Chadi.

 Minista a Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Mista Ibe Kachikwu ya bayar da sanarwar dakatar da aikin neman man fetur a Tafkin Chadi a watan Yulin da ya gabata, sakamakon kai harin da kungiyar ’yan ta’addan suka kai ga sojoji da masu aikin nemo man fetur din a yankin Tafkin Chadi.

Kamfanin NNPC ya fara nazarin farko kan neman fetur a Kogin Sakkwato da Magangarar Kogin Benuwai a watan Nuwamban shekarar 2016, kuma wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa yanzu kamfanin ya kara kaimi kan neman mai a kogunan Sakkwato da Benuwai da Bidda.  

Baya ga yankin Neja-Delta inda ake hako dimbin man fetur din Najeriya, an dade da tabbatar da cewa akwai man fetur da iskar gas a kogunan da suke Arewacin Najeriya da suka hada da Tafkin Chadi da Magangarar Kogin Benuwai da Kogin Sakkwato da na Bidda da kuma Kogin Arewacin Anambra.

Babban Manajan Daraktan Kamfanin NNPC, Dokta Maikanti Baru, ya tabbatar da hakan, lokacin da Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya ziyarce shi a Abuja a ranar Talatar da ta gabata.

Dokta Maikanti Baru ya ce tuni Kamfanin NNPC ya samu bayanan yanayin kasar Kogin Sakkwato ta hannun Hukumar Kula da Yanayin kasa ta Najeriya tare da bayar da kwangilar dada daddale samfurin abin da aka gano domin kara sanin yanayin yankin.

Ya bayar da sanawar cewa Kamfanin NNPC ya bukaci wani kamfani da ke karkashinsa mai sun Integrated Data Serbices Limited (IDSL), ya kara gudanar da wasu gwaje-gwaje don hadawa da tattara bayanan da suka kamata a samu a dora daga inda aka tsaya.

Da yake mayar da jawabi, Gwamna Tambuwal ya ce, Gwamnatin Jihar da hadin gwiwar Jami’ar Usman danfodiyo za su shirya wani babban taro na kasa kan Kogin Sakkwato a watan Oktoba domin bayar da tata gudunmawa a kokarin da ake yi wajen gano man fetur din a Kogin Sakkwato.

Wata sanarwa da Kakakin Kamfanin NNPC, Ndu Ughamadu ya fitar ta ce Gwamna ya ce, bisa bayanan da ake da su game da gano fetur din, sake ci gaba da neman man a kogin yana iya haifar da sakamakon mai kyau a nan kusa.

 A wata tattaunawa da Daily Trust a baya, Babban Manajan Kamfanin nema da hako man fetur na Frontier Edploration Serbices (FES) mallakar Kamfanin NNPC, Dokta Bako Mazadu ya ce fasalin yanayin kasa da bayanan da aka samu a kogunan Bida da Sakkwato za su ba kamfanin damar sanin yawan man da ke jibge a kogunan da kuma hasashen zurfinsa.

Wata majiya da ke Kamfanin IDSL ta ce tuni an nazarin farko kan wasu rijiyoyi da batun mazauna yanki da yanayi da kuma yiwuwar matsalar tsaro a kogin Kolmani da yankin Gombe da ke Magangarar Kogin Benuwai.

“Shirye-shirye sun yi nisa, amma Magangarar Kogin Benuwai ta fi nuna alamun samun man,” inji majiyar.