✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NNPC ya ba da izinin sayar da man fetur ba dare, ba rana

NNPC na shirin adana lita biliyan 2.3 na man fetur a cikin mako biyu masu zuwa.

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya ba wa manyan rumbuna da kuma gidajen mai izinin dako da kuma sayar da mai na tsawon awa 24 a fadin Najeriya.

NNPC ya ce umarnin na daga cin matakan da ya dauka domin shawo kan matsalar karancin man da ta addabi Najeriya a halin yanzu.

NNPC ta fitar ta kuma shawarci al’ummar Najeriya da su guji wahalar zuwa sayen mai saboda fargabar samun karancinsa, domin masu harkar mai sun fara aiki ba dare ba rana domin wadata ko’ina da man fetur.

Sanarwar ta kara da cewa tuni manyan kamfanoni da gidajen mai suka fara aiki da umarnin dako da kuma sayar da mai na tsawon awa 24 domin tabbatar da ya watada a kasar.

A cewar NNPC, yana shirin adana lita biliyan 2.3 na man fetur a cikin mako biyu masu zuwa.

Hakan, a cewarta zai tabbatar da samuwar wadataccen mai na tsawon wata guda a fadin Najeriya ba tare da wata tangarda ba.

An samu matsalar karancin mai a fadin Najeriya ne bayan NNPC ya shigo da gurbataccen mai kusan lita miliyan 100 a makon jiya.

Matsalar karancin man ta zo ne a daidai lokacin da dillalan mai suka yi barazanar shiga yajin aiki saboda shirin Gwamnatin Tarayya ta janye tallafin mai.

Daga baya dai gwamnatin ta dage lokacin janye tallafin man da wata 18.