Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta lakada wa ma’aikata duka cibiyar samar da wutar lantarkin duka sannan ta rufe tashar.
Wakilan NLC sun yi dirar mikiya a tashar babbar cibiyar ne da misalin karfe 1 na dare, inda suka fatattaki ma’aikatan, suka yi wa wadanda suma turken duka har wasu rauni, suka kora su, sannan suka kashe injian wutar cibiyar da ke Benin, Jihar Edo.
Kamfanin Samar da Lantarki na Ƙasa (TCN) ne ya yi wanna zargi a safiyar Litinin.
Sanarwar da Manajan Daraktan hulda da jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya sa wa hannu ta ce jami’an kungiyar kwadagon sun kai irin wannan farmaki tare da rufe tashoshin samar da wuta na Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da kuma Osogbo.
- Yajin aiki: Maniyyatan Najeriya na cikin rashin tabbas
- Jerin ’yan daban Kano 13 da ake nema ruwa a jallo
A cewar Mbah, hakan ya da dole aka bar wasu layukan samar da wutar a kunne.
Kazalika dole aka rufe daya da ciki tsahosin wutar lantarki na Jebba da masu wasu kanana guda uku saboda ba za su iya daukar karfin wutar ba.
Duk wadannan sun faru ne tsakanin karfe 1.15 zuwa 2.30 na dare.
Ya ce, sakamakon haka, da misalin 3.20 na daren TCN ta fara kokarin daidaitawa da dawo da wutar ta hanyar amfani da tashar Shiroro da kuma turawa ta layin Katampe, amma duk da haka NLC na kawo musu cikas.
Ya ce duk da haka za su ci gaba da yin iya bakin kokarinsu wajen ganin an dawo da wutar.
Kawo yanzu dai kungiyar kwadagon ba ta ce uffan kan wannan zargi ba.
Aminiya ta ruwaito cewa jami’an kungiyar na ci fa da rufe cibiyoyin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu domin tabbatar da yajin aikin da kungiyar ta kira.
A halin da ake ciki NLC ta tsayar harkoki cik a filin jirgi na Murtala Muhammad da ke Legas.
A Jihar Kaduna, jami’an kungiyar sun rufe harabar Jami’ar Jihar Kaduna (KASU).