Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwana 21 a kan ta kawo karshen yajin aikin da Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ke yi.
Rassan Kungiyar a fannin ilimi su ne suka bayyana haka a karshen taron da suka gudanar ranar Alhamis.
Cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Ayuba Wabba da kuma babban Sakatarenta na kasa, Emmanuel Ugboaja, NLC ta bukaci gwamnati da ta kafa wani kwamiti mai karfi wanda zai shiga tsakani domin samar da maslaha a cikin kwana 21.
Ta kara da cewa, idan gwamnati ta gaza yin abin da ya kamata har wa’adin da ta yanka mata ya kare, daga nan za ta yi taro domin sanin mataki na gaba da ya dace ta dauka.
Jami’o’in gwamnati a fadin Najeriya sun shiga wani hali tun bayan da ASUU ta tsunduma yajin aiki sama da watanni biyu da suka gabata saboda rashin biya mata bukatunta.