Wannan shi ne karo na shida da GIZAGO (08065576011) ke ci gaba da ninkaya da nazari cikin faffada kuma zuzzurfan Kogin Hikima da Fasahar Marigayi Malam Sa’adu Zungur, musamman ma ta hanyar bitar shahararren wakensa na “Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya? Akwai darussa da suka danganci zamantakewarmu ta yau da kullum a Arewa da Najeriya baki daya:
Ya jama’a, barkanmu da jimirin bibiyar wannan sharhi, inda muke nazarin baitocin mashahurin malamin falsafa, marigayi Malam Sa’adu Zungur, a mashahurin wakensa mai taken ‘Arewa: Jamhuriya Ko Mulukiya?’ wanda ya rubuta shekara 66 da suka gabata, inda yake mana nasiha, tambihi da gargadi dangane da al’amuran shugabanci, addini, zamantakewar rayuwarmu ta yau da kullum. A yau nazarinmu zai ta’allaka ne ga baitoci goma sha tara, kamar yadda na tsakuro su a nan kasa, daga mashahurin waken na Zungur.
Jama’are akwai su da shugaba,
Ya gane shu’unen duniya.
Gwambe su ma ai da Abubakar,
Adali ne ya shige tambaya.
Ya Daurawa, ku bi mai dubu,
Abdu mai zance da macijiya!
Ko Bawo yana shakka tasa,
Ya gaje tutar gaskiya.
Marigayi Abdu na Kadiri,
Can Hadeja muke musu ta’aziya.
Wa ya gaji maza su Nagwamatse?
Sarkin Sudanin gaskiya.
Kwantagora tana murna da shi,
Ibrahim ya shige tambaya.
A Ilori, Igala da Igbirra,
Gaisuwarmu gare su, alafiya!
Kabiyesi Abdulkadiri,
Ka rike tutarka ta gaskiya.
Atta attanmu guda biyu,
Daya Alhaji ne ba tambaya.
A Okene, Buraima ya ce da mu,
Ya san daraja ta Mulukiya.
Mun kira, ya Sarkin Malamai,
Ilimi da Sarautar duniya!
A Abuja yake kan yaduwa,
Zai sadu da Birnin Lafiya.
A kasar Kuza ga Sarkin Birom,
Rwang Pam ya dauki dawainiya!
Can a Binuwai ga Sarkin Jukun,
Aku ne na Wukari abin biya.
Ka ji sunaye na Sarakuna,
Lardi-Lardi ba tambaya.
Manufarmu mu bayyana danguna,
Na kabilu, ban da tsirariya.
Don akwai wasu ma a sarakuna,
Mun bar su da ayar tambaya.
Hakkin jama’a na kansu duk,
Su rike igiyarsa da gaskiya.
A wadannan baitocin, Malam Sa’adu Zungur ya maida hankali kan shugabanni da shugabanci, inda ya rika doka misali da tsarin Mulukiya da ke gudana a zamaninsa. Kai-tsaye ya rika ambato sunayen wadansu sarakuna na Arewa da yadda iyayensu da su kansu suke gudanar da mulkin al’umma. Ya ambaci Sarkin Jama’are, Sarkin Gwambe, Sarkin Daura, Sarkin Hadeja da Sarkin Sudan. Sauran sarakunan sun hada da na Kwantagora, Sarkin Ilori, Atta-Atta masu mulkin al’ummar Igala da na Igbira a Okene. Haka ya ambaci sunan Sarkin Lafiya, Sarkin Birom a Filato, wato Rwang Pam da Sarkin Jukun, Aku-Uka na Wukari. Babban makasudin ambatar wadannan sarakuna a nan shi ne, domin a jaddada muhimmancin mulki da masu mulki a cikin al’umma.
Bayan samuwar mulki da masu mulki, to wane irin mulki ne ke yin tasiri ga al’umma? Malam Zungur ya bayyana cewa, mulkin adalci da gaskiya shi ne sahihin mulki, wanda ke wanzar da zaman lafiya da ci gaba a cikin al’umma. A can baitocin baya, mun ji yadda Malam Zungur ya ambaci ilimi a matsayin ginshikin da ke karfafa masu mulki, tare da samar da sahihiyar rayuwa ga al’umma.
Mu duba baitin nan: “Jama’are akwai su da shugaba, Ya gane shu’unen duniya.” Hakan ke nuna mana cewa ilimi ga mai mulki bai tsaya ga iya karatu da rubutu ba, mai mulki sai ya kasance ya mallaki ilimin harkokin duniya da sha’anonin da ke gudana a ko’ina. Da irin wannan ilimi ne zai san halayen mutane mabambanta, ba mutanensa kadai ba. Da haka zai san yadda zai bullo wa baki da kan ziyarci kasarsa ko suke zaune tare da mutanensa.
Adalci, kamar yadda Malam Zungur ya ambata, al’amari ne babba ga mai mulki, domin kuwa shi ne ke samar da daidaito da kwanciyar hankali a cikin al’umma. Shi ne kuma ke kara wa mai mulki kwarjini da kauna daga talakawansa. Dalili ke nan Malam ya rika yi wa sarakunan da ya ambata a wadannan baitocin ishara da yadda sarakunan dauri, iyayensu suka yi nasarar mulki, domin sun kasance masu adalci da gaskiya a sha’aninsu na mulki. Me hakan ke nufi? Malam yana kira ga kowane mai mulki ya sanya gaskiya da adalci a lamuransa, yadda zai yi nasara, kamar dai yadda shugabannin baya suka yi.
Jarumta, kwazo, karfin hali na daga cikin siffofin shugaban da ke son ya yi nasarar mulki. Mu dubi wannan baiti: “Daurawa, sai ku bi mai dubu, Abdu mai zance da macijiya!” Mu kara da baiti na gaba, mai cewa: “Ko Bawo yana shakka tasa, Ya gaje tutar gaskiya.”
Hakan ke nuna mana cewa sai jarumi ne ke tabbatar da gaskiya, shi ke adalci ta hanyar kwato hakkin raunana daga masu karfi. Shi ne kuma ke da juriya wajen dawainiyar jama’a. Mu duba wannan baiti: “A kasar Kuza ga Sarkin Birom, Rwang Pam ya dauki dawainiya.” Hakan ke kara nuna mana cewa mulki fa nauyi ne, dawainiya ne, sai jarumi mai jimiri.
Kamar yadda na ce a baya, ilimi na daga abin da ke karfafa mai mulki. Ba mai mulki kadai ba, duk mai son nasarar rayuwa sai ya nemi ilimi. Mu dubi wannan baiti: “Mun kira, ya Sarkin Malamai, Ilimi da Sarautar duniya!” Sai dai kuma wane irin ilimi muke bukata? Kowanne, na addini da na zamani, amma wanda zai mana amfani a rayuwarmu ta yau da kullum. Domin kuwa wani masani mai suna Dokta John G. Hibben ya ce: “Ilimi shi ne samuwar ikon mallaka da sarrafa sha’anoni da tafiyar da al’amuran rayuwa.” Haka shi ma wani masanin, mai suna Herbert Spencer ya ce: “Babban kudirin ilimi bai tsaya ga mallakar sani ba, amma aiki da abin da aka sani.”
Malam Zungur dai a wadannan baitoci, ya daure masu mulki da jijiyar wuyansu, inda kuma ya nemi mu ma al’umma jimlatan mu nemi ilimi, mu gudanar da adalci da gaskiya cikin al’amuransu. Mu dubi baitocin nan: “Don akwai wasu ma a sarakuna, Mun bar su da ayar tambaya. Hakkin jama’a na kansu duk, Su rike igiyarsa da gaskiya.”
Da haka ne za a zauna lafiya a kasa, ba tare da wnuna kabilanci ba. Har ila yau dai, mulki nauyi ne mai girma, hakki ne abin kiyayewa ba ga masu mulki kadai ba, har da daidaikun jama’a. Maigida na dauke da hakkin iyalinsa, malamin makaranta na dauke da hakkin dalibansa, mace a gida na dauke da hakkin mijinta da na ’ya’yanta – dukkan wadannan shugabanci ne, hakki ne da ke bukatar kulawa da gaskiya da adalci. Allah Ya sa mu dace, amin.