✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote zai gina tashar jiragen ruwa mafi girma a Najeriya a jihar Ogun

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya mika takardun neman izinin gina tashar jiragen ruwa mafi girma da zurfi a fadin Najeriya a jihar…

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya mika takardun neman izinin gina tashar jiragen ruwa mafi girma da zurfi a fadin Najeriya a jihar Ogun.

Da yake tattaunawa da jaridar Bloomberg ta Birtaniya, attajirin na Afrika ya ce tuni ya aike da bukatar tasa domin fara aiki a gabar ruwa ta Olokola da ke jihar ta Ogun.

Ya ce gina tashar zai taimaka wajen saukaka fitar da kayayyaki waje daga Najeriya, ciki har da makamashin gas da kuma bunkasa rukunin masana’antunsa.

Ya ce tuni yunkurin nasa ya yi nisa inda tun a watan da ya wuce ya mika takardun neman amincewa da bukatar tasa.

“Ba wai so muke a ce mun mamaye komai ba, amma ina kyautata zaton yin hakan zai karfafa gwiwar sauran masu zuba jari su ma su zo su yi hakan,” in ji shi.

Gina sabuwar tashar dai nan una dawowar Dangote filin da a baya ya yi watsi da shi, bayan tun da farko a can ne ya kuduri aniyar gina matatar man shi da kamfanin sarrafa takin zamani, kafin sabanin da ya samu da mahukuntan jihar ya say a dakatar da shirin.

A karshen watan Mayun da ya gabata kamfanin na Dangote ya sanar da cewa yana hankoron samun Dalar Amurka miliyan bakwai a kullum daga sayar da takin zamani a nan da shekaru biyu masu zuwa.

Wata daya bayan haka kuma, ya sanar da far araba man dizal da na fetur a ranar 15 ga watan Agusta mai zuwa, inda tuni har ya kawo motoci masu amfani da gas guda 4,000 domin aikin rarraba man a fadin Najeriya.