Gwamnatin Sojin Nijar ta koro jakandan Najeriya a kasar Mohamed Usman, daga kasarsu.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijar ta umarci Mohammed Usman ya bar kasar cikin awa 48, a daidai lokacin da shugban kasar Najeriya Bola Tinubu ya tura malaman Musulunci domin tattaunawa da sojin da suka yi juyin mulki a Nijar.
- Kun yi kadan ku kori jakadanmu —Faransa ga sojojin Nijar
- Wata 1 da juyin mulki: Nijar ta kori jakadan Faransa
Karo na biyu ke nan Tinubu wanda shi ne Shugaban Kwamitin Shugabannin Kasasshen ECOWAS, ya tura malaman domin shawo kan sojojin, a yayin da ECOWAS ke tunanin amfani da karfin soji a kansu domin dawo da Shugaba Mohammed Bazoum kan kujerarsa.
Ma’aikatar harkokin wajen Nijar ta ce ta “Kori Jakada Mohammed Usman ne, saboda ya ki amsa gayyatar da ma’aikatar ta yi masa ranar Juma’a, da kuma wasu abubuwa da gwamnatin Najeriya ke yi da suka ci karo da muradun kasarsa, shi ya sa aka ba shi awa 48 ya bar kasar.”
Ma’aikatar ta kuma ba wa wa Jakadan Jamus a kasar, Olivier Schnakenberg, awa 48 ya koma kasarsa, bisa wadannan dalilai, kamar yadda ta sanar a cikin wata takarda ta daban.
Wannan dai shi ne dalilin da ma’aikatar ta bayar kan korar takwaransu na kasar Faransa, Sylvain Itte.
A ranar 26 ga watan Yuli sojojin rundunar tsaron shugaban kasar Nijar karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani, suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki.