✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kun yi kadan ku kori jakadanmu —Faransa ga sojojin Nijar

Faransa ta ce jakadanta da gwamnatin sojin Nijar ta kora ba zai matsa ko'ina ba.

Faransa ta nuna wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar yatsa bayan da suka kori jakadanta daga kasarsu.

Jim kadan bayyan gwamnatin sojin Nijar ta ba Jakadanta Faransa Sylvain Itte wa’adin awa 48 ya bar kasar, gwamnatin Faransa ta fito tana cewa sojojin ba su isa ba.

Sanawar da Ma’aikatar Harakokin Wajen Faransa ta fitar ta yi watsi da umarnin gwamnatin sojin Nijar, tana mai cewa sojojin ba su da hurumin korar jakadanta daga Jamhuriyar Nijar.

A ranar Juma’a sabon Ministan Harakokin Wajen Nijar CNSP, Bakary Yaou Sangaré, ya ba wa Mista Itte awa 48 ya tatttara nasa ba bar kasar.

Gwamnatin Nijar ta ce ta kori Jakadan Faransa daga kasar ce bayan da Bakary ya gayyace shi dan tattauna wani batu, shi kuma ya ƙi zuwa.

Sanarwar ta kara da cewa kafin bijirewar jakadan da ta kora, kasar na nuna wasu take-take da ke barazana ga al’ummomin Nijar.

Sojojin dai na zargin Faransa da sakin ’yan ta’adda da aka kama, da kuma saba dokar hana bi ta sararin samaniyar kasar.