✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wata 1 da juyin mulki: Nijar ta kori jakadan Faransa

Gwamnatin sojin Nijar ta ba wa jakadan Faransa wa'adin awa 48 ya fice daga kasar

Gwamnatin sojin Nijar ta korji jakadan Faransa Sylvain Itte, wata guda bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum, babban abokin Faransa.

Ma’akatar harkokin wajen Nijar ta sanar da ba wa jakadan Faransan wa’adin awa 48 ya tattara kayansa ya fice da kasar.

Sanarwar ma’aikatar ta ce an kore shi ne saboda kin amsa gayyatar da gwamnatin Nijar ta yi masa, da kuma “take-taken gwamnatin Faransa da suka ci karo da manufofin Jamhuriyar Nijar.”

Ta zargi jakadan da kin zuwa tattauna a kan dalilin rashin saukar tsohuwar Jakadiyyar Nijar daga mukaminta bayan an bata umarni da kuma ganawarta da Ministan harkokin wajen Faransa.

Gwmanatin sojin ba ta yi karin haske ba kan sauran take-taken na Faransa, amma a baya ta zargi sojojin Faransa da sakin ‘yan ta’addan da aka kama, da kuma bi ta sararin samaniyar Nijar da aka haramta musu, wanda ta ce barazana ce ga al’ummar Nijar.

Wata guda ke nan kasashen duniya da kungiyoyin ECOWAS da AU suna neman ganin sojojin sun koma bariki sun mika wa Bazouma kujerarsa; inda kasashen ke barazanar amfani da karfin soji idan masu juyin mulkin sun yi taurin kai.

ECOWAS da AU da manyan kasashe duniya sun yanke hulda da Nijar suka kuma sa mata takunkumi a sakamakon juyin mulkin, wanda ya sa manyan kasashen duniya janye tallafin da suke wa matalauciyar kasar, majalisar dinkin duniya kuma ta dakatar da aikin agajinta.

Gwamnatin sojin Nijar dai na zargin ECOWAS da hada sojojinsu da na wasu kasashe baki da ba ta bayyana ba.

Kafin juyin mulkin na watan jiya dai Nijar na dasawa da Faransa, tsohuwar uwar dakinta. Amma kifar da gwamnatin Bazoum ke da wuya ssojoji da wasu al’ummar Nijar suka nemi Faransa ta fice daga kasar.

Faransa na da dakaru 1,500 a sansanin sojinta da ke Nijar, inda take taimaka wa gwamnatin Bazoum wajen yaki da ‘yan ta’adda; amma sojoji da wasu ‘yan Nijar na zargin Turawan da taimkon ‘yan ta’addan.

A yayin da kasashen duniya ke ta kokarin ganin an dawo da Bazoum ko da ta karfin soji ne, sojojin suka hambarar da shi  sun samu goyon bayan kasashen Mali da Burkin Faso wajen yakar duk kasar da ta kawo hari Nijar.

Tun kafin nan, shugaban gwamnatin sojin , Janar Abdourahmane Tchiani, ya ce duk kasar da ke tunanin shiga Nijar da karfin soja, za ta gane kurenta idan ta yi.

A ranar Alhamis ya yi wata ganawa da ministocin kasashen kasashen Burkin Faso da Mali ke hannun gwamnatin soji, inda ya sa hannu kan dokar ba wa sojojinsu izinin kawo wa kasarsa dauki idan aka kawo mata farmaki.

Mako guda ke nan bayan Janar Tchiani ya sanar cewa Burkina Faso ta girke jiragen yaki, domin yakar duk wani hari da ake shirin kawo wa Nijar.

A makon da ya gabatan ne dai gwamnatinsa ta fara daukar sojojin sa-kai da take shirin amfani da su, idan ta kama, an kawo mata hari.