Gwamnatin Sojin Nijar, ta sanar da cewa ranar 26 ga watan Yuli za ta zama Ranar ’Yancin ƙasar.
Wannan ita ranar da sojoji suka kifar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, a shekarar 2023.
- Tarihin Najeriya ba zai zama cikakke ba da na faɗi zaɓen 2023 — Tinubu
- ’Yan sanda sun bankaɗo maɓoyar IPOB a Imo, sun ƙwato makamai
Wannan bayani ya fito ne daga wata majiyar kafar watsa labarai ta Air Info Agadez.
An ce gwamnatin sojin ta ayyana ranar ne domin tunawa da juyin mulkin da sojojin suka yi, wanda ya kawo ƙarshen mulkin Bazoum.
Kwamitin ministocin Nijar, ya ce za a gudanar da bukukuwan ranar ta musamman da saukar Alƙur’ani da addu’o’in neman zaman lafiya da albarkar damina.
Wannan saukar za ta gudana a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli.
Haka kuma gwamnatin ta buƙaci jama’ar ƙasar su riƙa yi mata addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaba.
An kifar da Bazoum ne a ranar 26 ga watan Yulin 2023, a ƙarƙashin jagorancin shugaban mulkin soja Abdourahmane Tchiani.