Jamhuriyar Nijar da ƙasar Rasha a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 sun ƙulla yarjejeniya game da makamashin nukiliya da kuma haƙar yuraniyom.
Kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP) ya ruwaito cewa ƙasashen biyu sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce bayan ganawar shugaban Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, da wata babbar tawagar Rasha ƙarƙashin jagorancin Ministan Makamashi, Mista Sergei Tsivilev.
- Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China
- Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma
“Muhimmiyar manufarmu ita ce mu ƙara inganta rayuwar mutanen Nijar da na Rasha,” in ji Sergei, kana ya bayyana cewa sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya game da makamashin nukiliya da haƙar yuraniyom.
“Mun amince cewa za mu horar da manyan jami’ai waɗanda za su iya aiki a fannonin tallafinmu irin na makamashi da noma da lafiya da ilimi, kuma za mu horar da injiniyoyi tun a makarantu domin su ci gaba da karatunsu a jami’o’in da ke Tarayyar Rasha,” in ji shi.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan dangantaka tsakanin Tarayyar Rasha da Nijar, in ji rahoton na ANP.
Bayan ganawar dai Ministan na Rasha ya bayyana godiyarsa ga shugaba da mutanen Nijar domin irin tarbar da aka yi masa.
“Mun ga bayanai da dama game da damarmakin da ke akwai a cikin Nijar, kuma a halin yanzu mutanenmu na ƙoƙarin aiki kan damarmakin da ke nan a Nijar,” in ji Mista Sergei Tsivilev, wanda shi ne shugaban ɓangaren Rasha a hukumar haɗakar gwamnatoci da ƙasashen AES.
“Shugaban ƙasar ya kuma sanar da mu cewa shi zai zaɓi shugaba na ɓangare ɗaya na hukumar haɗakar gwamnatocin nan ba da jimawa ba domin ayyukanmu da ‘yan uwanmu na Nijar su yi ta tafiya babu tangarɗa,” in ji shi.