A yayin da Najeriya ke bikin cika shekara 62 da samun ’yancin kai, wani masani kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum a jihar Katsina ya ce sam gwamnati mai ci ta gaza wajen cika alkarunta, musamman a bangaren tsaro.
A zantawarsa da Aminiya albarkacin zagayowar samun ’yancin kan, wanda shi ne zai kasance na karshe a wa’adin mulkin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Sarkin Fukanin Dankama, Alhaji Ishak Sarkin ya ce akwai Buhari zai ta fi ya bar Najeriya da tarin kalubale.
- Babu abin da zai wargaza Najeriya —IBB
- Majalisar Dattawan Amurka ta amince a ba Ukraine tallafin Dala biliyan $12
Sarkin Fulanin, wanda tsohon ma’aikaci ne kuma marubuci ya ce hatta jiharsa, wacce daga cikinta ne Shugaban Kasan ya fito, ci baya ta samu ba gaba ba a wadannan shekarun.
Sai dai ya ce abin da kawai za a ce an dan samu saukin shi ta fannin tsaro a kasar shi ne daina kai harin bama-bamai a kasuwanni da wuraren ibada da sauran wuraren taruwar jama.
Gwamnati ta gaza
A cewarsa, “Kundi Tsarin Najeriya ya ba kowane dan Najeriya dama ta gwamnati ta kare masa rayuwa da dukiya da kuma mutunci da sauran abubuwa a matsayin damar da yake da ita.
“Amma sai ga shi a yau kowane sashe na kasar nan wasu tsirarun mutane suna salwantar da rayuka, jini da dukiya da muhalli da mutuncin ’yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, ba su aikata laifin komai ba.
“Wasu an kai su daji, wasu cikin gidajensu wanda aiwatar da hakan ya saba wa sassan Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ya ba kowane dan kasa ’yancin rayuwa,’yancin addini, fadin albarkacin baki, mallakar dukiya, mutuntawa, zama a muhalli, zirga-zirga da walwala da sauran irin su.
“Abin tambaya a nan shi ne, a ina ake samun duk wadannan abubuwa a yanzu a Najeriya, musamman Arewacinta?” inji shi.
‘Ilimi ma baya ya ci’
Sarkin Fulanin ya ci gaba da cewa hatta da batun samar da abubuwan more rayuwar da kundin ya bayyana sai da cikakken tsaro ake samunsu.
Masanin ya ce hatta bangaren ilimi rikicin bai bari ba, saboda yana daga cikin bangarorin da aka fi illatawa.
“A lura da kyau, idan gwamnati na son kashe mutanenta ta mayar da su bayi to ta hana su ilmi.
“Ya zuwa yau din nan [2022], akwai jami’o’i akalla 170, cikinsu 43 na gwamnatin tarayya, 48 na jihohi yayin da sauran 48 na ’yan kasuwa. Duk ma ba wannan ba, babbar illar yanzu ita ce, an yi wa batun ilimin kofar rago, a hannu guda kuma ’yan ta’addan daji sun hana samar da ilmin a yankunan da suke da bukatar shi sosai.
“A daya bangaren kuma ga yajin aikin malaman jami’o’i da aka kwashe akalla wata bakwai a yanzu ana yi ba tare da samun wata kwakkwarar hanyar kawo karshen shi ba,” inji shi.
Da wakilinmu ya tambaye shi ko shekara 23 din da aka yi ba tare da katsa-landan din sojoji ba shi ma nasara ne, sai mai sharhin ya ce, “Na san wasu za su ce haka, amma kada a manta da cewa, ai mulkin farar hula ake yi a Najeriya ba na Dimokuradiya ba.
“Mulkin da ake cewa ka-ci zabe alhalin ba ka ci ba, dorawa ake yi. A kasar da za a ce an yi zabe a cikin jiha wai jam’iya mai mulki ita ce ta cinye duk wasu kujerun da aka yi takara ba tare da samun ko guda daga bangaren masu hamayya ba, akwai alamun tambaya,” inji shi.