✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni ne zan lashe zaben 2023 —Tinubu

Tinubu, ya bayyana kwarin gwiwarsa na lashe zaben shugaban kasa

Dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ya bayyana kwarin gwiwarsa na lashe zaben shugaban kasa da ke gudana a ranar Asabar.

Tinubu ya sanar da haka ne bayan da ya kada kuri’a a mazabarsa da ke Jihar Legas tare da mai dakinsa, Sanata Oluremi Tinubu.

Bayan ya kada kuri’ar tasa ce a rumfa mai lamaba 85, gunduma ta 3, a Alausa, manema labari suka tambaye shi ko zai taya wanda ya yi nasara a zaben murna idan bai kai bantensa ba.

Budar bakin Tinubu ke da wuya, sai ya ce, ai “Ni ne zan lashe zaben”, cikin kwarin gwiwa.