✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ni da Masari sam ba ma iya barci saboda matsalar tsaro – Sarkin Katsina

Sarkin ya ce matsalar tsaron ta sa ba sa iya barci da ido biyu a Katsina, shi da Gwamna.

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya shaida wa Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo cewa da shi da Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari, sam ba sa iya barci da ido biyu saboda kalubalen tsaron da ya addabi Jihar.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga Mataimakin Shugaban Kasar, wanda ya kai masa ziyarar ta’aziyya, saboda rasuwar mahaifiyar attajirin nan, Alhaji Dahiru Mangal ranar Lahadi.

A cewarsa, “Wannan zuwan naka a karon farko tun da ka fara yakin neman zabe zuwa ne mai cike da tarihi a wajenmu. Yanzu a gida kake, kuma ka yi magana a kan matsalar tsaro, wadda ita ce babbar matsalar da ta dame mu.

“Ban jima da dawowa daga Kaduna ba, inda ina zuwa na iske kusan kiran waya 100 a kan wani shiri da ’yan ta’adda ke yi na kai hari, wanda a yanzu ya zama ruwan dare.

“Ni da Gwamna Masari, ba mu da wani lokacin da muke iya yin barci da idanunmu biyu a rufe, amma na yi matukar farin ciki da aka ayyana wadannan miyagun a matsayin ’yan ta’adda,” inji Sarkin.

Tun da farko dai a nasa jawabin, Farfesa Osinbajo ya ce ya yi matukar murna da ya ji an ce yanayin tsaron Jihar na dada inganta, kamar yadda Masari ya shaida masa.

“Shugaban Kasa ya tattauna da dukkan kwararru a sha’anin tsaro kuma za a yi canji a inda ya kamata don a samu ingantuwar tsaro a fadin kasa.

“Ko a kwanan baya, idan mai martaba zai iya tunawa, Shugaban Kasa ya ba da umarnin a ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, domin a ba jami’an tsaro damar murkushe su.

“Muna sa ran ganin ci gaba, kuma da yardar Allah zaman lafiya zai dawo ba wai a yankunan Jihar Katsina kawai ba, har ma da Najeriya baki daya,” inji Mataimakin Shugaban Kasar.

Tun da farko dai sai da Osinbajo ya fara zuwa gidan Mangal din domin yin ta’aziyyar, kafin daga bisani ya isa fadar sarkin.