Bunun Katsina na I Alhaji Salisu Ado Shinkafi ya bayyana cewa shi ne mutum na farko da aka fara nadawa sarautar Bunu a Masarutar Katsina.
Ya ce Bunusarauta ce wadda ake yi a duk inda sarakuna fulani suke mulki. Sai dai kuma Bunun yace,wanda bai shafi sarauta ba ne in an ba shi yake jin wani abu.
“To ni yanzu haka mahaifina ne ke Magajin Garin Modoji. To ka ga ashe na tashi a cikin harkokin mulki na gargajiya sannan kuma ga na gwamnati. Sai dai kuma duk da haka,wannan sarauta ta janyo mani ƙarin huɗɗa da sarakuna saboda duk inda na shiga in aka ce ga ni, to za ka ga ana maraba da ni tamkar sarkin ne ya zo. Na ga haka a wakilcin da na yi a wani naɗi da aka yi a masarautar Katagum,” inji shi.
Bunun ya ja hankalin matasa da suka riƙa neman sanin muhimmancin sarautunmu na gargajiya domin su ne suka kusantar al’umma fiye da kowane irin shugabanci. Amma sai ka ga wasu suna wasa da sanin sarauta wai saboda yarinta,sai in hankali ya zo sannan kuma za a ce a neme ta. Bunun Katsina ya ƙara da cewa, kowane al’amari na duniya yana da irin nasa matsalar kuma wannan matsalar ita ce ci gaban abin ko mene ne.
An haifi Alhaji Salisu Ado a ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar 1951 a garin Shinkafi. Ya yi makarantar firamare daga 1957 zuwa 1963 a tsakanin makarantar Kayalwa da kuma ta Rafindaɗi dukkansu da ke cikin garin Katsina. Ya shiga Kwalejin Gwamnati da ke garin Funtuwa a tsakanin 1964 zuwa 1968, sai kuma makarantar Kimiya da Fasaha ta Kaduna daga 1971 zuwa 1974, inda ya samu takardar sheda a kan abin da ya shafi sha’anin mulki. Kazalika, ya ƙara ɗaga darajar takardar shaidar ta shi zuwa difuloma a nan dai wannan makaranta.
Ya fara aikin gwamnati a matsayin Mataimakin Jami’in jin daɗi da walwala a yankin Arewa ta tsakiya har zuwa Babban Jami’in daga 1970 zuwa 1987. Daga nan ya zama Jami’in Hukumar Alhazai a Ƙaramar hukumar Mani. A haka likkafa ta yi ta ci gaba har zuwa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida a matsayin Mataimakin Darakta wanda kuma ya ajiye aiki a 2002.
Duk da ajiye aikin da ya yi, bai sa an ƙyale shi don ya huta ba saboda Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta ɗora masa nauyin kula da jihohin Arewa maso yamma tun daga shekarar 2007 zuwa 2015 inda ya faɗa harkokin siyasa bayan ya rabu da wannan hukuma. A yanzu haka shi ne Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai na Jihar Katsina, wanda Gwamna Masari ya naɗa shi.
Ya zama Bunun Katsina na farko wanda Mai martaba Sarkin Katsina Dokta Abdulmuminu Kabir Usman ya naɗa a ranar 31 ga watan Maris na 2012.
Ita dai wannan sarauta na daga cikin irin sarautun aro da sarakuna kan yi a tsakaninsu. Sarautar Bunu ta samo asali daga Adamawa. Kalmar Bunu wadda ta fito daga harshen Fulatanci tana nufin dangantaka da jama’a a masarauta, ko a ce na kusa ko aminin sarki kuma na jini. Duk mai riƙe da wannan matsayi na Bunu a gidan sarauta, to zai iya shiga tsakani a duk lokacin da aka samu wata matsala a tsakanin sarki da ‘yan uwansa ko na kusa da shi. Ke nan sarauta ce wadda ta jiɓanci ‘ya’yan sarki. Amma dai babban muhimmin abu ga wannan sarauta shi ne, mai shiga tsakani ne tare da bayar da shawara ga sarki. Har ila yau, yana wakiltar sarki a duk inda sarki bai samu damar zuwa ba.
Kamar yadda wasu bayanan suka nuna, Bunu na iya riƙe masarauta a lokacin da sarki baya nan. A wasu masarautun kamar Bauchi, Bunu shi ne mai bai wa sarki shawara a tsakaninsa da iyalansa. Shi ke ƙoƙarin ganin an samu kyakkyawar tarbiya, ɗa___’a da ladabi da biyayya. Yana daga cikin amintattun sarki kuma mai taimakawa sarki a wajen shawo kan wasu matsaloli na yau da kullum musamman ga abin da ya shafi iyalai da dangi. Kusan irin wannan aikin ne Bunu ya kanyi a masarautar Sakkwato. A wasu masarautun kuma,Bunu na riƙe Hakimci.