✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ngon: Matar da ta shekara 41 tana shan ruwa kadai

Ta nisanci dukkan sauran abubuwan gina jiki.

Wata mata ’yar kasar Vietnam ta yi ikirarin cewa, ta bar cin abinci mai tauri sama da shekara 40 da suka gabata kuma tana rayuwa a kan ruwan da aka sa masa gishiri da sukari da ruwan lemon tsami tun daga lokacin.

Matar mai suna Misis Ngon mai shekara 63 ta shahara a yankinta na Tan Trach da ke Lardin Long na kasar Vietnam, saboda irin cimarta.

Shekaru 41 da suka wuce, ta gano cewa tana rayuwa a kan ruwa da wasu ‘yan giram na gishiri da sukari da kuma dan lemon tsami kadai, inda ta nisanci dukkan sauran abubuwan gina jiki.

Jikinta, ya yi mulmul duk kuwa da shekarunta, sannan kuma tana cikin koshin lafiya da kuzari.

Haka kuma, tana iya aiwatar da nau’o’in motsa jiki na Yoga, wadanda masu yawan shekaru ba za su yi mafarkin yi ba.

Ngong tana atisayen motsa jiki na Yoga

Ngon ta daina cin shinkafa da sauran kayan abinci masu nauyi lokacin da ta kai shekara 21, ta fara fuskantar matsalolin lafiya, inda ta ringa lalacewa, cikinta yana zafi kuma kullum sai ta yi amai.

Gwajin koshin lafiyarta ya nuna cewa, tana fama da wata cuta a jini.

Ngon tana atisayen motsa jiki na Yoga

Bayan ta yi kokarin shan maganin da aka ba ta tare da ganin lafiyarta ta inganta, sai ta yanke kauna da ci gaba da rayuwa.

A lokacin ne ake zargin wani likita ya ba ta shawarar ta fara shan ruwan da aka hada da gishiri da sukari ta daina cin abinci mai nauyi.

Ya ce mata za ta iya matse ruwan ‘ya’yan itace idan ta so.

Likitan ya tabbatar mata cewa, idan ta bi wannan sirrin da ya ba ta sau da kafa, zai taimaka mata ci gaba da rayuwa, kuma watakila ma ta warke daga cutar jininta.

Sai dai ya yi mata kashedin da kada ta taba bayyana sunansa, domin abun bai dace da ilimin kimiyya ba, kuma mutane za su rika sukarsa.

Matar ta cika alkawari, inda ta ki bayyana wa kowa sunansa.

Abu daya da za ta iya cewa shi ne, shawararsa ta yi aiki, inda ita kanta shaida ce.

Duk da haka, ba ta ba wa wani shawarar cin abu mai ruwa kadai ba, saboda ta yarda cewa yana iya zama hadari.