✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF za ta biya sabon kocin Eagles Naira miliyan 16 a wata

Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta fara shirin dauko sabon koci daga waje wanda zai maye gurbin Samson Siasia kuma ana sa ran …

Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta fara shirin dauko sabon koci daga waje wanda zai maye gurbin Samson Siasia kuma ana sa ran  za ta rika biyansa albashin Dala dubu 50 kwatankwacin Naira miliyan 16 ne a duk wata.
Wannan albashi da za a rika biyan sabon kocin ya ninka wanda aka biya Stephen Keshi da Sunday Oliseh a lokacin da suka jagoranci kungiyar.
Tsohon kocin Kwaddebuwa  Herbe Renard da na Kamaru Paul Le Guen da kuma na Uganda Micho na daga cikin wadanda suka nuna sha’awar horar da kungiyar  Super Eagles.
A makonnin baya ne dai aka ruwaito Shugaban Hukumar NFF Mista Amaju Pinnick yana fadin akwai yiwuwar Samson Siasia ne zai kasance koci na karshe da zai horar da Super Eagles daga gida.  Hakan ya nuna hukumar ba za ta sake ba wani dan kasa dama ya zama kocin kungiyar ba, sai dai a rika daukowa daga waje.
Amma wannan kalami na shugaban  ya bata wa kungiyar kococin Najeriya rai, inda ta ce akwai yiwuwar ta umarci  membobinta su janye daga yi wa kungiyoyin kwallon kafa na kasa a mataki daban-daban aiki tun da ya nuna ba su da muhimmanci.
kungiyar ta ce ta lura hukumar NFF tana amfani da su ne wajen cin moriyar ganga amma ta yarda kwaure.
kungiyar ta ce ba ta ga dalilin da zai sa a rika dauko hayar koci daga waje ana biyansu makudan kudi ba alhali daga cikinsu akwai wadanda za su iya yin abin da kococin waje suke yi.
kungiyar ta ce abin takaici ne yadda ake ba kococin waje fifiko fiye da na gida, da hakan ya sa ake kashe musu kwarin gwiwa.
Sai dai NFF ta nuna ba yanzu za ta dauki sabon kocin ba sai an gama wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afirka da Masar a ranakun 25 da kuma 29 ga wannan wata da muke ciki a garin Kaduna da kuma wasa na biyu a can Masar.
Masana harkar kwallo suna ganin dauko sabon koci daga waje ba shi ne mafita ba ga koma-bayan harkar kwallon kafa a Super Eagles.  Wasu na ganin yin haka tamkar barnar dukiya ce musamman a wannan lokaci da gwamnati ke kukan rashin isassun kudi.