Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF), ta sallami kocin tawagar ’yan wasan Super Eagles Augustine Eguavoen da mukarrabansa, kwana biyu bayan gaza samun tikitin zuwa gasar Kofin Duniya ta 2022 a za a yi a Qatar.
Sakatare-Janar na hukumar, Dokta Mohammed Sanusi ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa, inda ya ce hukumar ta janye kwantaragin shekara biyu da ta bai wa Eguavoen.
- Mun gaji da gafara sa kan matsalar tsaro – Malaman Kaduna ga Buhari
- ’Yan bindiga sun fara tuntubar iyalan wadanda suka sace a harin Kaduna
“Biyo bayan gaza zuwa gasar kofin duniya da Super Eagles ta yi na 2022, an sallami Augustine Eguavoen daga mukaminsa kuma hukuncin zai fara aiki nan take.
“NFF ta janye kwantaragin da ta bai wa kafatanin tawagar kocin na shekara biyu, kuma nan take za su ajiye aikinsu,” a cewarsa.
Sanusi ya ce nan gaba kadan za a sanar da sabbin tawagar da za su jagorancin tawagar ’yan wasan Super Eagles don ta sake dawowa kan ganiya da kuma goyayya a harkar kwallon kafa.
“Mun gode wa daukacin tawagar kocin bisa gudunmawar da suka bai wa kasar nan, muna musu fatan alheri a rayuwarsu.”