✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NFF ta fara zawarcin ’yan kwallon Arsenal biyu

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce tuni ta tuntubi iyalan ’yan kwallon Arsenal da ke Ingila su biyu masu suna Chuba Akpom…

Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa (NFF) ta ce tuni ta tuntubi iyalan ’yan kwallon Arsenal da ke Ingila su biyu masu suna Chuba Akpom da Aled Owobi don ganin sun buga wa Najeriya kwallo a matakin manya.

Su dai ’yan kwallon an haife su ne a Najeriya amma tun suna kanana iyayensu suka koma Ingila da zama, al’amarin da ya sa suka yi wa Ingila kwallo a matakin yara yanzu kuma Najeriya take zawarcinsu don su yi mata wasa a matakin manya.
Hukumar ta ce tuni shugaban Hukumar NFF Mista Amaju Pinnick ya ziyarci Ingila inda ya gana da iyalan ’yan kwallon don ganin ya shawo kansu a kan yiwuwar su bar ’ya’yansu su yi wa Najeriya kwallo a matakin manya.
dan shekara 18 Aked Owobi an haife shi ne a Legas amma iyayensu suka koma Ingila. Ya yi wa Ingila wasa a matakin yara kuma yanzu haka yana daga cikin ’yan kwallon da za su wakilci Ingila a gasar wasanni ta Olamfik. Shi ma Chuba Akpom a Legas aka haife shi amma iyayensa suka canza sheka zuwa Ingila a lokacin yana karami. Yanzu dukkan ’yan kwallon suna buga wa kulob din Arsenal kwallo ne a matakin manya.
A ranar Lahadin da ta wuce shugaban NFF din ya ziyarci filin wasan Arsenal inda ya kalli wasan cin kofin kalubale (FA) a tsakanin Arsenal da na Middlesbrough kafin ya zarce gidajen iyayen nasu don ganawa da su.