✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NEMA ta raba kayan abinci ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Borno 

An raba wa wadanda lamarin ya shafa don rage musu radadin da suke ciki.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta bayar da gudunmawar tan 400 na kayan abinci ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno. 

Shugaban hukumar ta NEMA, Alhaji Mustapha Ahmed, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da kayayyakin ga Shugabar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA), Hajiya Yabawa Kolo a Maiduguri.

Muhammad Kanar wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan kula da ma’aikata na NEMA, Ahmed ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bayar da tallafin domin rage radadi ga wadanda abun ya shafa.

Ya ce an yi hakan ne domin a taimaka wa wadanda abin ya shafa don rage musu radadin da suke ciki, domin hukumar ba za ta iya mayar wa mutanen abin da suka rasa ba.

Ya lissafa kayayyakin wanda hada da buhu 1,000 na shinkafa, buhun wake 1,000, buhun masara 1,000, buhun gishiri 75 da sauran kayan amfanin yau da kullum.

Shugaban na NEMA, ya ce tana da rahoton iftila’in ambaliyar ruwa a kananan hukumomi sama da 450 da ke fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, lamarin da ya janyo asarar rayuka, dukiyoyi da ababen more rayuwa.

Ahmed ya ce lamarin ambaliyar ruwan da aka yi a baya-bayan nan da aka samu a kasar, ya yi kira da a dauki matakai don rage hadarin ambaliyar da ta haddasa asarar rayuka.

“Wannan ya yi daidai da burin duniya na rage faruwar iftila’i.

“Don samun damar cimma wannan, muna bukatar mu samu kyakkyawar fahimta game da hadarin ambaliya, ta hanyar zurfafa nazari.”

Da yake mayar da martani, Kolo ya yaba wa shugaban kasa kan yadda ya tallafawa wadanda abin ya shafa a lokacin da ya dace.

Ta ce ambaliyar ta raba mutane da gidaje 37,000 tare da lalata gonaki 67,000 a kananan hukumomi 14 na jihar, inda ta kara da cewa matakin zai rage illar ga wadanda abin ya shafa.

%d bloggers like this: