Shugaban Hukumar Gudanar da kungiyar kwallon kafa ta Neja Tornadoes Malam Adamu Aliyu Muhammad ya sanar cewa sun kammala duk tanade-tanaden da suka kamata domin ganin an biya ‘yan wasa da jami’ansu hakkokinsu kafin a fara kakar wasa ta bana. Ana sa ran za a fara kakar wasan ce a ranar 20 ga wannan wata da muke ciki.
Malam Adamu Aliyu Muhammad ya sanar da haka ne a wata takarda da Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar Mista George Daniya ya sanya wa hannu inda Aminiya ta ci karo da ita.
Ya bayyana gamsuwarsa game da yadda ‘yan wasan kulob din ke samun horon da ya dace da kuma yadda aka tantance ‘yan wasan da suka nuna sha’awar yi wa kungiyar wasa a rukunin kwararrun da za a fara a wannan watan da muke ciki.
Ya ce lokacin yi wa ’yan kwallon rikon sakainar kashi ya wuce, inda ya tabbatar da cewa za a kula da su a kakar wasa mai zuwa don ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Da ya juya kan jita-jitar da ake ta yayata wa cewa wasu mutane suna kokarin yi wa shirin tunkakar kakar wasa mai zuwa kafar inda suka nemi kocin kungiyar ya cusa sunayen wasu ‘yan wasan da bai san da su ba .Ya ce ba haka al’amarin yake ba, ya ce an ba Kocin damar ya zabo tare da tace ’yan wasa 30 wadanda yake ganin za su yi masa wasa a kakar wasa mai zuwa kuma an ba shi wuka da nama don ganin an samu biyan bukata.
A karshe ya shawarci jama’a da su rika binciken al’amuran da suka shafi kungiyar musamman ‘yan jarida wadanda suka taka muhimmiyar rawar da ta sa kungiyar da jami’an gudanar da ita samun nasarori a kankanen lokaci.Ya tuna musu cewa bai kamata su rusa dangantakar da aka dade ana ginata cikin lokaci kankane ba.
Neja Tornadoes za ta biya hakkokin ’yan wasanta kafin a fara kakar wasa ta bana
Shugaban Hukumar Gudanar da kungiyar kwallon kafa ta Neja Tornadoes Malam Adamu Aliyu Muhammad ya sanar cewa sun kammala duk tanade-tanaden da suka kamata domin…