Hukumar Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar da dalibai masu kammala marantar sakandare suka zana a watan Yulin 2021.
Shugaban NECO, Farfesa Dantali Wushishi, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, Jihar Neja ranar Juma’a.
- Buhari ya ce ko an kara mishi wa’adin mulki ba zai karba ba
- ’Yan bindiga sun karbi sigari a matsayin fansar mutum takwas
Ya ce daga cikin dalibai 1,233,631 da suka yi rajistar jarabawar, an tabbatar da dalibai 1,226,631 da suka zana jarrabawar.
Wushishi ya kuma bayyana cewa dalibai 945,853 ne suka samu kiredit biyar da suka hada da darussan Ingilishi da Lissafi, dalibai 1,094,291 kuma suka samu kiredit biyar babu Ingilishi ko lissafi a ciki.
Ya ce adadin daliban da suka samu kiredit biyar da suka hada da Ingilishi da Lissafi ya kai kashi 71.64 cikin 100, idan aka kwatanta da sakamakon jarabawar na 2020.
Wadanda suka samu kiredit biyar babu Ingilishi ko Lissafi kuma kaso 94.04 ne cikin 100, idan aka kwatanta da na 2020 da ke da 91.9 cikin 100.
Wushishi, ya ce an kama dalibai 20,003 da laifin aikata satar jarabawa a 2021, sabanin 2020 da aka samu dalibai 33,470 da laifin.
Sannan ya kara jadadda hukuncin hukumar a duk lokacin da aka dalibi na satar amsa a yayin zana jarabawar.
Ya ce dalibai za su iya duba sakamakon jarabawarsu a intanet.