Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kama wani fitaccen mai hada maganin nan da ake yi wa lakabi da ‘A Kurkura’ da kwalabe 26,600 na maganin.
A baya dai hukumar ta haramta sha da sayar da maganin saboda yadda ta ce akwai mau’in sa maye a cikinsa.
- NAJERIYA A YAU: Yanka 11 Na Gani A Jikin Ummita —Mai Wankan Gawa
- Wadanne shugabannin duniya aka gayyata bikin binne Sarauniya Elizabeth II?
Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA na kasa, Femi Babafemi ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Lahadi, inda ya ce an kama mutumin ne ranar 13 ga watan Satumban 2022.
Ya ce wani jami’in hukumarsu ne ya kama shi da tarin kwalaben da ake kokarin raba su a fadin jihohin Arewacin Najeriya.
Ya ce an kama kayan ne a daidai Gadar Tamburawa da ke kan hanyar Kano zuwa Zariya a jihar Kano.
Ya ce daga bisani hukumar ta sami nasarar cafke mamallakin kayan, wanda dan asalin karamar hukumar Akinyele ta jihar Oyo ne, tare da wasu dilolinsa su uku bayan fadada bincike. (NAN)