Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta kaddamar da kwamitin sassa daban-daban don yaki da zamba ta Intanet.
An bukaci kwamitin ya tsara yarjejeniya kan matsayar da masu ruwa-da-tsaki kan harkokin zambar kudi ta amfani da kafofin sadarwa suka cimma.
Yarjejeniyar tana daya daga cikin matsayar da masu ruwa-da-tsaki kan zambar kudi ta hanyoyin sadarwa suka cimma a taron da suka gudanar a ranar 29 ga Janairun bana.
Da yake jawabin maraba, a wajen taron kafa kwamitin, Shugaban Hukumar (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya ce sakamakon cimma kashi 35.4 na amfani da Intanet, ’yan ta’adda da ’yan dandatsa da masu kutse da sauran miyagu suna amfani da kafar wajen cutar da mutanen da ba su san hawa ko sauka ba, ta hanyar shiga asusun ajiyar bankuna ta haramtacciyar hanya ta hanyar kutse da sauran dabarun da suke kitsawa kamar musayar layin wayoyi da zagaye tsarin tantancewa, ya alla an gudanar da hada-hadar ta wayar hannu ce ko kwamfuta ’yar tebur ko ta tsarin POS.
Farfesa Dambatta ya ce masu kula da abokan hulda da masu kula da harkokin zamba a bankuna da ta tarhi suna bukatar manya da kuma tsauraran matakai kan yadda za su gano yiwuwar aukuwar ayyukan zamba kuma su biya wadanda aka zambata a inda dabarun rigakafi suka gaza aiki. Ya ce hukumar tana aiki da manyan masu ruwa-da-tsaki kamar Babban Bankin Najeriya (CBN)m da Rundunar ’Yan sandan Najeriya da Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Tu’annati cin (EFCC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) da sauran hukumomin da suka dace, don aiwatar da dabarun da hanyoyin samar da maslaha kan wannan fanni.
Shugaban na NCC ya ce kwamitin zai bullo da hanyar aiwatar yarjejeniyar wadda a cewarsa za ta samar da hanyar ta’asa ta Intanet sosai. Ya ce cikakkiyar hada gwiwa a tsakanin hukumomin gwamnati da kamfanonin ’yan kasuwa ce kashin bayan dakile karuwar wannan zamba ta kafafen sadarwa.
“Kasancewar haka a rai, ya sa aka natsa sosai wajen zabo wakilan wannan kwamiti don su yi amfani da kwarewarsu wajen samar da nasara kan wannan muhimmin aiki. “Abin da muke fata daga gare su yana da yawa, kuma muna sa ran samun cikakke kuma sakamakon da ya tabo kowane gefe daga kwamitin,” inji shi.
Tubn farko da take tofa albarkacin bakinta wajen bude taron, Daraktar Harkokin Abokan Hulda ta Hukumar NCC, Misis Fecia Onwuegbuchulam ta ce kafin samuwar kungiyar masu ruwa-da- tsakin, tu’annatin zambar kudi ta amfani da tarho ko sadarwa ya yi gauni inda ya shafi kusan kowane bangare da sassan masana’antar.
Ta ce matsalar ta’addancin Intanet ta wuce asarar dimbin kudi har ma tana matukar zubar da mutuncin masu kamfanonin tarho da bankuna da ita kanta Hukumar NCC da CBN da hukumomin tsaro da ita kanta kasar nan.
Ta ce, “Hukumar ta sha karbar korafe-korafe kan zambar kudade ta amfani da hanyoyin tarho ko sadarwa, kuma sakamakon haka ne ta shiga nemo hanyoyin wayar da kan jama’a kan batun da kuma yadda za a magance aukuwar hakan. Kwamitin masu ruwa-da-tsaki na daya daga cikin tsare-tsaren da hukumar ta bullo da su don samar da ingantattun sharwarwari da mafita ga wannan matsala.”
Kwamitin ya kunshi Bankin CBN mutum biyu, Hukumar NCC mutum biyar, bibbiyu daga Hukumar Gasa da Kare Abokan Hulda ta Tarayya da Kwamitin Sasanta Bankun daHukumar Katin Dan Kasa da Kungiyar Masu Lasisin Gudanar da Tarho (ALTON) da wakilan bankuna uku da hukumomin tsaro da Ma’aikatar Shari’a.