✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna

Osasuna na zargin cewa ɗan wasan baya na Barcelona, Inigo Martinez wanda ɗan asalin Sifaniya ne, bai cancanci buga wasan ba.

Akwai yiwuwar Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa wata dokar Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) a wasan gasar La Liga wanda ta doke Osasuna.

Rahotanni na cewa ƙungiyar Osasuna za ta shigar da ƙorafi kan wasan da Barcelona ta doke ta da ci 3-0, saboda zargin saɓa dokar FIFA kan amfani da ɗan wasan da bai cancanta ba.

A jiya Alhamis ce Barcelona ta karɓi baƙuncin Osasuna a wani kwantan wasa na gasar La Liga, inda to doke baƙin nata da ci 3-0.

Wannan nasarar ta bai wa Barcelona damar yin zaman faɗi da tazarar maki 3 a saman teburin La Liga da jimillar maki 63, bayan buga wasanni 28.

Sai dai wasan ya bar baya da ƙura, saboda Osasuna na zargin Barcelona ta karya wata dokar FIFA kan amfani da wani ɗan wasa yayin karawar.

Osasuna na zargin cewa ɗan wasan baya na Barcelona, Inigo Martinez wanda ɗan asalin Sifaniya ne, bai cancanci buga wasan ba.

A kakar bana, tauraruwar Martinez na haskawa tun bayan zuwan sabon koci Hansi Flick ƙungiyar, wanda ya sa ɗan wasan ya samu kiranye daga tawagar ƙasarsa Sifaniya a watan nan.

Sai dai ɗan wasan ya samu rauni a gwiwa, lamarin da ya tilasta masa baro tawagar Sifaniya da ke buga gasar UEFA Nations League, inda aka maye gurbinsa da ɗan wasan Bournemouth, Dean Huijsen.

Sai dai kuma bayan ya baro tawagar ta Sifaniya, Martinez ya dawo ƙungiyarsa ta Barcelona, inda ya buga wasan da suka yi nasara kan Osasuna a ranar Alhamis.

Shafin Goal ya ambato wata jaridar wasanni ta Sifaniya, Diario Sport, na cewa Osasuna na duba yiwuwar shigar da ƙorafi kan Barcelona saboda zargin taka dokar FIFA dangane da saka ɗan wasan da ya baro tawagar ƙasarsa.

Osasuna na ganin cewa, bai kamata a ce Martinez ya buga wasan ba saboda dokar FIFA ta ce ‘yan wasan da suka baro tawagar ƙasarsu ba za su buga wa ƙungiyarsu wasa ba har sai bayan aƙalla kwanaki biyar, face idan hukumar ƙwallo ta amince masa ya buga