Kimanin mutum 150 ne suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wasu munanan girgizar ƙasa daban-daban da suka auku a ƙasashen Myanmar da Thailand.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa girgizar ƙasar wadda ta auku a wannan Juma’ar ta jikkata ɗaruruwan mutane a yayin da baraguzai suka danne gommai.
Hukumar binciken yanayin ƙasa ta Amurka (USGS) ta bayyana cewa an fuskanci wata mummunar girgizar kasa har kashi biyu masu ƙarfin awo 7.7 da 6.4 a Myanmar, tare kuma da wata girgizar ƙasar mai karfi da ta yi ɓarna a kasar Thailand wacce ta shafi wasu wurare a yankin.
Girgizar ƙasa ta farko ta afku ne a wani wuri mai nisan kilomita 16 a arewa maso yammacin birnin Sagaing wacce ta mamayi aƙalla kilomita 10 da misalin ƙarfe 12:50 na daren ƙasar ranar Juma’a, a cewar hukumar binciken yanayin ƙasar ta Amurka USGS.
Gwamnatin ƙasar da za ta gudanar da bincike kan lamarin cikin gaggawa tare da fara ayyukan ceto da kuma samar da kayayyakin agajin jin kai, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Telegram.
A cewar wasu shaidu biyu daga garin Taungnoo da ke yankin Bago da suka zanta da kamfanin dillancin labaru na Reuters, aƙalla mutane uku ne suka mutu bayan wani ɓangare na wani masallaci ya rufta.
Girgizar ƙasar ta yi kaca kaca da cibiyar kasuwancin Bangkok haɗi da tituna da gadoji da kuma wani dogon gini mai hawa 30 da ko kammala shi ba a yi ba.
Tuni dai Firaministan Thailand, Paetongtarn Shinawatra ya ayyana dokar ta ɓaci a Bangkok.
Haka kuma, sojojin da ke mulki a Myanmar sun sanar da ayyana dokar ta ɓaci a babban birnin da kuma birni na biyu mafi girma a ƙasar da wasu jihohi shida.