Aƙalla mutum 122 ne, suka rasa rayukansu bayan wani jirgin sama ɗauke da fasinjoji 181, ya kama da wuta yayin da yake sauka a birnin Muan, da ke Koriya ta Kudu.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya fara yin gararamba kafin ya kama da wuta kuma ya tarwatse.
- Tinubu na ɓoye wa ’yan Najeriya gaskiyar halin da ƙasa ke ciki — Sule Lamido
- Abba ya tarbi ɗaliban Kano 150 da suka kammala digiri na biyu a Indiya
Hotunan da aka wallafa sun nuna yadda hatsarin ya kasance.
Masana harkar sufurin jiragen sama, sun ce akwai yiwuwar matsalar injin jirgin ce ta haifar da lamarin.
An ceto mutum biyu kawai daga cikin tarkacen jirgin, waɗanda dukkaninsu ma’aikatan jirgin ne.
Sai dai masu aikin ceto sun ce ba sa tunanin za a samu sauran rayayyun mutane daga hatsarin.
Tun farko, Hukumar Kashe Gobara ta ce mutum 85 ne suka mutu, ciki har da mata 46 da maza 39.
Amma daga bisani adadin ya ƙaru zuwa 122.
Jirgin saman, wanda mallakar kamfanin Jeju Air ne, ya taso daga Bangkok na ƙasar Thailand tare da fasinjoji 175 da ma’aikata shida, kafin ya yi hatsari a filin jirgin sama na Muan.
Jirgin, ƙirar Boeing 737-800, ya kasance cikin matsala yayin sauka, wanda ya yi sanadin wannan mummunan hatsarin.