✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Girgizar ƙasa ta hallaka sama da mutum 1000 a Myanmar

Gwamnatin ƙasar ta nemi ɗauki daga ƙasashen duniya game da girgizar ƙasar.

Gwamnatin Soji ta Myanmar, ta bayyana cewa mutum 1,002 sun rasa rayukansu sakamakon girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta auku a ranar Juma’a.

Sama da mutum 2,000 sun jikkata, kuma ana ci gaba da ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin gine-ginen da suka rushe.

Jami’an agaji sun ce girgizar ƙasar ta fi shafar birnin Mandalay, inda asibitoci suka cika maƙil da waɗanda suka jikkata.

Shugaban mulkin soji na Myanmar, ya nemi taimakon ƙasashen duniya, amma ana fargabar yaƙin basasa da ke ci gaba a ƙasar zai hana ayyukan jin-ƙai tafiya yadda ya kamata.

Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce Myanmar na cikin yaƙi tun shekaru huɗu da suka wuce, wanda ya haifar da zargin cewa dakarun soji na tsare ɗaruruwan mutane.