Daga abin da muka gani a can baya, muna iya cewa adawa da kushe da tashin-tashina da ce-ce-ku-ce da shiga cikin rumbun adabi domin samun galaba da goyon baya da kuma kafa gwamnati ba sabon abu ba ne. Ba Rarara ya fara ba, ba kuma kansa za a tsaya ba. Wannan kuwa ya zame haka ganin cewa abin ya samo asali ne cikin tarihi, sai kuma an bi tarihin a tsanake za a ga yadda wainar ta toyu. Abin da za mu kokarta yi ke nan daga yau.
Mu sani tun farko duniyar siyasar Arewacin Najeriya ta kasance bisa tagwaitattun al’amurra ne da jam’iyyu biyu suka ja ragama kai, wato NEPU da NPC. Kowace daga cikin jam’iyyun suna da magoya baya da kuma tsarin da suke bi da kuma manufofi ko akidoji. An kuma yi amfani da wake da zambo da kirari da habaici da zambo-zagi domin isar da sako da cin dunduniyar juna a siyasance.
Domin ganin yadda da’irar adawar Arewacin Najeriya ta kasance tsakanin NEPU da NPC a wancan lokaci, wadannan baitoci da suka yi tashe a wancan kokaci sun isa misali, NPC da magoya bayanta na cewa:
“Sarki da alkali duk namu ne,
Kowa ya zage mu bulaliya.”
Su kuma ’yan NEPU suka dinga mayar da martani ta hanyar fadar:
“Allah da Manzonsa duk namu ne,
Kowa ya zage mu sai hawiya.”
Daga irin bayanan da ke cikin wadannan baituttuka an fahimci cewa lallai dokin sugar ’yan NPC tare da taimakon ’yan mulkin mallaka ya haye kan ’yan NEPU ba kaukautawa. An yi haka ne kuma ba tare da jin tsoro ko neman boye manufa ba. A wata wasikar da sakataren Gwamnatin Arewacin Najeriya ya sa wa hannu a 1954, an bayyana a fili irin yadda hukuma ta dauki wadannan ’yan adawa. ’Yan NEPU da farko dai an yi kira ga En’e-En’e su sani cewa ire-iren wadannan ’yan adawa na NEPU da suka yi wa lakabi da “cinnaku” yawancinsu “suna da tabon taba karya doka, ba kuma yadda za a yi a rabu da su in ba an yi musu feshin sheltos ba, hakan kuma ba zai faru ba sai “an karya doka da taushe hakkinsu.”
Domin a sanya takunkumi a bakunan wadannan ’yan adawa, sai aka shiga soke rijistar kungiyoyin da suke tattaruwa kansu, wadansu aka sa su yin hijira, wadansu aka hana jama’a hulda da su, wasu aka hana su amfani da kayan gwamnati wajen tarurrukansu. Irin wannan kisan mummuke Sarkin Bauchi Adamu ya yi amfani da shi wajen soke kungiyar ci Gaban Jama’ar Bauchi. Bai dai ce kada a ci gaba da gudanar da kungiyar ba, amma da ji an san manufarsa. Ya ce da Sa’adu Zungur da su Malam Aminu Kano “ba wanda ya ce kada ku yi tarurrukanku, sai dai abin da ba ya bisa ka’ida shi ne ku yi amfani da kayan gwamnati ko kuma a lokacin aikin gwamnati domin gudanar da tarurrukanku. Ta haka aka bi aka dinga jefa ko aza shingaye gaban ’yan adawa, wanda kuma shi ya haifar da abin da aka kira tashin-tashina a fagen siyasar Arewacin Najeriya.
Kila tambayar da wadansu za su yi a nan ita ce, me ya sa wasu jan daga da ’yan mulkin mallaka da danniya a Arewacin Najeriya? Turjiya ga wanda aka zalunta ko nuna adawa ga gwamnati, musamman wadda ta kauce hanya abu ne ginanne a cikin zukatan al’ummar Arewa. Tun kafin Jihadin Usumanu danfodiyo, har da ma lokacin jihadin da bayan kammala jihadin, an sha samun masu ganin jinjiri a bayan uwarsa su tambayi wane ne mahaifinsa; irin su Bakin Wake (kafin jihadi), malaman ’Yandoto (zamanin masu jihadi), malaman Satiru (zamanin zuwan Turawa) duk za su iya zama kyakkyawan misali. Haka kuma yakin duniya na biyu ya kara bude idanun mutanen Arewa dangane da yadda duniya take ciki. Sojojin da suka halarci fagen fama sun dawo gida da tunanin lallai ’yanci na da dadi. Tare da taimakon ’yan siyasa da suka yi karatu mai zurfi game da gina kasa da tattalin arziki sai aka shiga zafafa tunani da tattuna matsaloli da kuma bijire wa duk wadansu abubuwan zalunci da danniya, wanda hakan ya kawo ka-ce-na-ce da tashin-tashina.
Wani abin la’akari a nan shi ne, ayyukan assha da aka yi wa ’yan NEPU da sauran ’yan adawa ba su tsaya ga soke rijistar kungiyoyinsu ba, sun hada da kame da daurin karya, bugu da kisan kai, wannan ne ya sa a can garin Hadeja ake yi wa alkalin garin kirari:
“Ya alminjir maganin ’yan NEPU, daure mai gaskiya don maras gaskiya ya ji tsoro.”
Ta amfani da kotu da alkalai da ’yan doka aka dinga kuntata wa ’yan adawa. Ila Ringim da danjani Hadeja, daure su aka yi a jikin dawakai, aka bugi dawakan da karfi suka dinga jan su a kasa, tun daga Sabon Garin Mai ’Ya’ya har cikin birnin Kano, ba don komi ba, sai don sun halarci taron siyasa ba tare da famit ba. A Wasu kuwa an yi musu yadda aka yi wa Musulman farko a Makka, aka matsa musu sai sun yi riddar siyasa daga NEPU zuwa NPC, musamman wadanda aka kai gaban sarkin Kano na wancan lokaci. Wannan ya sa ’yan adawa da dama suka gwammace su je gaban kotunan Turawa a maimakon kotunan Shari’a (alkalai) idan suna da matsala da wani ko wasu, domin kuwa a gaban alkalin Sarki ba a tambayar bahasi, ba beli, sai dai dauri kawai ga dan NEPU.
Ba wannan kadai ba, a can kauyuka an matsa wa talakawa su bayar da hatsin kambi. Wasu magidanta kuwa an sa su dole su gina shararra ne daidai inda gidajensu suke, daga wannan kauye zuwa wancan ta amfani da kayan aikinsu da abincinsu, dogarai na biye suna zagayawa, suna yi wa malalaci bulala in ya nemi ya huta, wanda ya nemi ya yi tsiwa ko rashin kunya nan take za su buge, su daure, domin su aikinsu bai wuce hushi da hushin wani ba. Haka kuma ga bala’in nan na noman gandun sarki, ga biyan kudin ushira (gado) ga kwana da matan talaka ko ’yan adawa a duk lokacin da dagaci ko hakimi ya kai ziyara wasu sassa na kasarsa, ko kuma a yi shela a kai amarya gidan uban kasa kafin a kai ta dakin mijinta.
Daga shekarar 1954 lokacin da NPC ta soma mulki a Arewa, ’yan adawa ba su ji dadi ba, Lawal Dambazau ya jaddada haka, inda yake cewa, daga wannan shekara jam’iyyar NPC ta shiga yaki da talakawa, duk wanda ya ki goya wa jam’iyyar baya sai ka ga an cinno masa sarakuna ko alkalai ko ’yan doka su yi masa yaga-yaga. Su kuma malamai da daliban addini tuni aka yi musu nuni da cewa ai jam’iyyar NPC jam’iyya ce ta Shehu Usumanu danfodiyo, don haka su ’yan NEPU da magoya bayansu duk kafirai ne. A yawancin lokuta an sha kai hari gari (don kame) kamar yadda ake harin bayi, wasu aka kai gidan yari, wasu aka yi musu dukan tsiya, wasu aka washe musu gidaje, wasu aka lalata sana’arsu ko kayan sana’a, kamar gonaki, wasu aka kwace musu mata, wasu suka ma rasa rayukansu.
Ganin irin wannan rayuwa ta kunci da tashin hankali da talakawa ko kuma ’yan adawa suka shiga, ya sa wadanda aka kai ga bango sukan yi kukan kura, sukan nemi mafita. Tun da yake ba su da goyon bayan hukuma, ba su da alkalai ko ’yan sanda, sai yawancin ’yan NEPU suka shiga mayar da martani ta hanyar da suka san hukuma ba za ta iya hanawa ba. Da farko dai suka kulla kawance da jam’iyyar NCNC, wadda a wancan lokaci tana da jaridu masu yawan gaske da take amfani da su wajen fada da ’yan mulkin mallaka da masu goya musu baya.
Abin la’akari a nan shi ne, ko a wancan lokaci jaridun da ake da su a Arewacin Nijeriya na hukuma ne, Gaskiya Ta Fi Kwabo da aka kafa a 1939 domin farfagandar yakin duniya na biyu aka asassa ta. Tun daga shekarar 1954 kuma Gwamnatin Arewa ta samar da jaridu na Larduna, ta yadda zuwa shekarar 1956 kusan kowane Lardi na da tasa jaridar, kai har inda ma ba a amfani da harshen Hausa an kafa musu tasu. A Lardin Kano inda nan ne hedikwatar ko mazaunin NEPU, jaridar Sodangi da Daily Mail su ne tambarin NPC wajen farfaganda. Ta amfani da wannan jarida da hukumar mulkin mallaka da jam’iyyar NPC suka shiga yada karya game da NEPU da magoya bayan jam’iyyar. Sa’annan kuma hukuma ta tabbatar ba a ba ’yan adawa damar amfani da jaridun ba, balle a ji ta bakin ’yan adawa. Duk wani aikin ci gaba ko wani abu da hukuma ta san zai sa NEPU ta sami tagomashi ko goyon baya to ba a sa shi a cikin jaridun Sodangi da Daily Mail.
Dangane da haka, abu na farko da jam’iyyar NEPU ta fara nema daga kawancenta da NCNC shi ne a sama musu wurin da za su dinga maida martani game da farfagandar hukuma da jam’iyyar NPC. Wannan ya sa aka samar da wani wuri na musamman a cikin jaridar Daily Comet a Kano, aka kebe wani bangaren jaridar domin dimbin masu karantun Hausa, domin sun riga sun san cewa fargaganda ta fi armashi a cikin harshen da mutane ke fahimta. Da kafuwar Daily Comet a Kano sai rawa ta canza, wanda ke kan doki sai ya koma kan kuturi, wannan ya bayar da dama aka shigo da siyasar mayar da martani ta Yankan Kunkurun Bala.
Za mu ci gaba
Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (4)
Daga abin da muka gani a can baya, muna iya cewa adawa da kushe da tashin-tashina da ce-ce-ku-ce da shiga cikin rumbun adabi domin samun…