Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne da shiri da kuma tsarin da Turawa suka yi kafin su bar Arewacin Nijeriya da ma Najeriya baki daya. Sanin yadda hakan ya faru na da muhimmanci, saboda ta haka ne za a gane yadda tuyar masar yau da Rarara ya aza ta kasance.
A lokacin da Turawan Birtaniya suka auka wa kasar Hausa daga shekarar 1903, suka yi awon gaba da Daular Usumaniya, sun yi haka ne da niyya, domin su ga cewa sun tabbata a bisa gadon mulkin Arewa da ma sauran sassan Najeriya. Turawa ba su zo Arewa a makance ba, domin sun yi nazarin tsarin da za su iske, saboda haka da zuwa sai suka kyautata sassan da suka dace da manufofinsu, suka yi wa sassan da ba su dace ba kwaskwarima, wannan shi ya jawo amfani da sarakuna a nasu mulkin, wadanda suka bijire daga cikin sarakunan, suka yi waje-rod da su ba tare da bin tsarin ko tanadin da gargajiya ta samar ba ba, saura da suka gagara, aka karkashe.
Nufin Turawan mulkin mallaka shi ne su ga sun share duk wadansu alamun bore da turjiya a tsakanin al’ummar Arewa, sai dai ba su samu nasara ba, yaki da bijire wa ayyukan zalunci da danniya da aka san jama’ar Arewa da su ba su kau nan take ba, wanda shi ya jawo jan daga a wadansu Larduna na Arewa. Haka ya faru ne domin shekara 100 da Daular Usumaniya ta yi a daron kasa ta taimaka wajen gina jama’a masu tsoron Allah da kyamar zalunci da cin amana da rashawa, don haka akwai gyauron ire-iren wadannan jama’a ko da Turawa suka kunno kai suka amshe mulkin Arewa, shigowar su ma ya samar da wani sabon faifai ne na hada-hadar siyasar mulkin mallaka.
Kodayake Turawa ba su sami yadda suke so ba baki daya, amma sun ci nasara wajen kafa gwamnati ta munafinci a kaikaice. Sun dai bar tsarin mulkin da suka iske, amma sun kasa, sun tsare. Sarakai da hakimai da dagatai kowa ya rike mukaminsa a karkashin sabon tsarin sarakuna, sai dai Gwamna da Razdan da Di’o su ke a sama. Da yake tsarin En’e ya amince da sarakuna, ya kuma amince da gado a matsayin hanyar hawa sarauta ba zaben nagari ba, sai wadansu sababbin matsaloli suka sake kunno kai daga shekarun 1930 lokacin da kawunan jama’a suka soma wayewa sosai saboda yakin duniya da wasu suka halarta daga Arewa da shigowar ilmin zamani da kuma yawan tafiye-tafiye da wasu suka yi, suka sami bude idanusu game da hakkin dan Adam a harkokin siyasa. Dayani da aka san Arewa da shi a matsayin tsarin falsafa tuni ya rushe, nan take aka soma samar da kungiyoyi ko kuma ra’ayoyi da za a iya kasa su zuwa gida biyu, akwai masu “ra’ayin rikau,” wato wadanda ke goya wa En’e baya, wannan gungu ya hada da sarakuna da tajirai da malamai, burinsu shi ne su ga an mika mulki daga hannun ’yan mallaka (Turawa) zuwa ga ’yan mallaka (na gida) bayan samun ’yancin kai, ba tare da wani canji ba. kungiya ta biyu ko kuma a ce masu ra’ayi daban da wannan su ne za a kira da ’yan “neman canji,” wadanda su kuma burinsu a kawo sauyi ko ta wace irin hanya, musamman daga abin da aka saba zuwa wani sabo, kuma mai ma’ana. Ga ’yan wannan kungiya, masu ra’ayin hukumar En’e da kuma sarakuna da masu mulki tare da Turawa, “sun butulce wa Musulunci ne,” wannan ya sanya suka shiga babatu game da mulkin danniya da zalunci da sarakuna ke yi tare da taimakon hakimai da dagatai da kotunan alkali da ’yan sanda, su kuma Turawa suka goya musu baya ta fuskoki daban-daban. Haka abin ya dinga gudana har zuwa lokacin da aka samar da kungiyoyi da jam’iyyun siyasa.
Ko kafin hakan ta samu ana da manunai da ke alamta cewa lallai za a sami shan daga tsakanin tagwaitattun jama’ar Arewa, hakan ya samo asali daga ra’ayoyi da littattafai da suka zama abubuwan dogara wajen canza da kyautata tunanin jama’a tun kafin zaman tare ya watse. Misali, a shekarar 1944 aka samar da kungiyar siyasa ta farko, wato kungiyar ci Gaban Arewacin Nigeriya (NGIU), a cikin wannan kungiya akwai jama’a mabambanta ra’ayoyi kamar su Abubakar Imam da Wazirin Zazzau da Malam Julde da Malam Jumare, da R.A.B. Dikko da John Garba da Sarkin Zazzau Jafaru da Razdan da Di’o da wasu gaggan jama’a da dama da ke zaune a Zariya. Wannan kungiya ba ta dade ba ta wargeje saboda dalilai masu dama. Na daya, zaman tare don tattauna batutuwa inda ake dauke da sarki da majalisarsa da Razdan da Di’o da wadansu ma’aikatan gwamnati bai yi wa gwamnati dadi ba, kingin kiris da wasu sun rasa mukamansu. Na biyu, tunani da ra’ayoyin wadansu daga cikin ’yan kungiyar ya saba ko kuma ya yi wa saura fintinkau, daga ciki akwai irin su Sa’adu Zungur wanda ke ganin cewa ba a yi wa mata adalci ba, musamman a harkar neman ilmi. Wannan “tsageranci” da wasu irin su da dama suka jawo aka rushe kungiyar, aka tarwatsa masu tada-zaune-tsaye irin su Sa’adu Zungur, aka tura shi Anchau wai ya yi yaki da kudan tsando.
Soke rijistar wannan kungiya bai hana an ci gaba da yaki da danniya ba, musamman bayan kammala yakin duniya na biyu (Yakin Hitla). Daga Lardin Bauchi (inda Sa’adu Zungur ya koma da zama a 1946) saboda rashin lafiya, zuwa Lardin Sakkwato da Katsina da Zariya aka shiga ka-ce-na-ce a cikin shafukan jaridun Gaskiya Ta Fi Kwabo da Jaridar Daily Comet da Daily Mail, a wannan lokaci an tattauna abubuwa da suka shafi kyamar da ’yan Arewa suka nuna game da zuwa yakin Hitla, ko zuwa hakar kuza a kwazazzabon kasar Fitato da kuma koke-koke kan yadda Turawa ke kwashe hatsin da ake nomawa a Arewa aka kai wa sojoji da ke fagen yaki.
Yawancin ire-iren wadannan koke-koke, gwamnatin mulkin mallaka ba ta yi saurin hana aukuwar su ba, sai ma ta kara taimaka masu. Razdan-Razdan na Larduna da dama sun taimaka musu ta hanyoyi daban-daban, musamman ta ba su shawara su kafa kungiyoyin gama-kai da taimakon juna. Wannan dama ce wadansu suka yi amfani da ita suka samar da kungiyoyin siyasa a kaikaice, a can Bauchi (BGIU). A Zariya an samar da kungiyar Zumunta, a Sakkwato kuwa aka samar da kungiyar Walwala ta Matasan Sakkwato, da kungiyar ’yan kasa ta Lardin Kano da sauransu.
Hada-hadar siyasa irin ta jam’iyya ba ta kankama ba sai daga karshen shekarun 1940, kuma su wadannan jam’iyyun siyasa sun samo asali ne daga iren-iren wadancan kungiyoyin gama-kai da aka ambata a baya. Ita dai Jam’iyyar Mutanen Arewa (NPC) har zuwa 1951 ta kunshi hadakar kungiyoyi da suka hada da Jam’iyyar Mutanen Arewa da Jam’iyyar Jama’ar Arewa da kungiyar Mutanen Bauchi da kungiyar Zumunta ta Sakkwato da kuma kungiyar ’yan kasa ta Kano.
Ita dai Jam’iyyar NPC manufarta da farko ba ta wuce yaki da jahilci da lalaci da zalunci ba, haka kuma da rusa majalisar sarakai ta Arewa, da ba mata dama su shiga majalisa da kuma shiga zabe da yin gyaran fuska ga hukumar En’e ta dace da zamani. Wannan ne ya sa da farko ake jin cewa jam’iyyar NPC ta kasance jam’iyyar neman sauyi da neman ci gaba da bacin shugabanni da ’yan mulkin mallaka, wannan ne ya sa da farko aka hana jami’an gwamnati shiga cikin jam’iyyar.
Ita kuma Jam’iyyar NEPU ta samo asali ne daga kungiyoyi biyu masu kama da juna. kungiya ta farko ita ce gyauron ’yan neman canjin da suka baro NPC bayan kaddamar da jam’iyyar a 1951, sai kuma uwar kungiyar ta asali wato NEPA, wadda aka kafa tun a 1946 da niyyar hada kan jama’ar Arewa da kuma bayyana wa jama’a cewa mutunen Arewa sun yi shiru ne game da harkokin siyasa ba wai don sun gamsu da abin da ke faruwa ba. Dangane da haka ne za a iya cewa NEPA tun azal ba ta da wani haufi na inda ta sa gaba, ba ta kaunar tsarin mulkin mallaka da kuma sarakunan da suka daure masu gindi.
Ganin irin turbar da NEPA ta dauka game da harkokin siyasa sai Razdan na Kano ya nemi ya san abubuwa da suka hada da (1) Manufar kungiyar (2) Yawan ’yan kungiyar (3) Da kuma yawan kudaden da kungiyar ke da su a daidai shekarar 1947. Rashin amincewa da bayanan da suka bayar, ganin kuma irin abubuwan da kungiyar ke takalowa, musamman game da lalataccen tsarin mulkin mallaka, ya sa hukuma ta rushe kungiyar a shekarar 1949. A shekarar 1950 sai NEPU ta kunno kai.
Jam’iyyar NEPU ta sha bamban da jam’iyyar NPC ta kowace irin fuska, burin NEPU shi ne ci gaba inda NEPA ta tsaya: Ciyar da tattalin arzikin kasa gaba da kuma fitar da talaka daga kangin bauta, musamman na Turawan mulkin mallaka da sarakuna. Bambancin wadannan jam’iyyau biyu ya kara fitowa fili daga shekarar 1951, ta fuskar wadanda suka kasance magoya bayansu da irin dangantakar jam’iyyun da sarakuna ko masu mulki. Ita dai NPC tuni ta watsar da shigar burtun da ta yi na neman zama jam’iyyar canji ta koma jam’iyyar danniya, wadanda suka shige ta ba su wuce ma’aikatan gwamnati da ma’aikatan fadojin sarakuna ba. Shi ya sa a Lardin Sakkwato da Adamawa yawancin ma’aikatan En’e su ne magoya bayan NPC, wata sa’a ma ba a bambantawa tsakanin shugabannin En’e da majalisar sarakai a bangare guda da kuma shugabannin NPC.
A nata bangaren jam’iyyar NEPU, jam’iyya ce ta “talakawa,” shugabanninta da magoya bayanta ba su wuce malaman makaranta ba, sai manoma, da ’yan garuwa da masunta da majema da madinka da masu faskare. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa NEPU ta zama jam’iyyar adawa, ta shiga Allah-wadai da danniya da tsarin mulkin mallaka da mulukiya, wannan shi ya jawo rashin jituwa tsakanin NEPU da hukuma. Gwamnati na ganin cewa maganar da NEPU ke yi ta hada kai tsakanin jama’a masu ra’ayi iri daya a Arewa da Kudu zai iya tada zaune-tsaye. Saboda haka sai gwamnatin danniya ta mulkin mallaka ta shiga shirya da tsara hanyoyin da za su sanya NPC ta gaje ta ba NEPU ba. An murgude sakamakon zabe, an ba NPC rahotannin musamman ta yadda za a ci dunun NEPU, aka kuma shiga ba ’yan doka da alkalai damar da za su kame su daure ba mai cewa ahir. Aka dinga nuna wa NPC dokokin da za su yi amfani da su, su tamke ’yan NEPU ba tare da wani ka-ce-na-ce ba.
Nazari: Mawaki Rarara da yankan kunkurun Bala (3)
Dukkan wadannan abubuwa sun faru ne da shiri da kuma tsarin da Turawa suka yi kafin su bar Arewacin Nijeriya da ma Najeriya baki daya.…