✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiru Gawuna ne ya ci zaɓen Gwamnan Kano -Kotu

Kotun ta soke ƙuri'u 165,663 daga cikin na Abba, kuma ta umarci Hukumar INEC ta janye shaidar nasarar da ta miƙa masa.

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta ayyana Nasiru Gawuna na Jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano.

Kotun ta soke ƙuri’u 165,663 kuma ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta janye shaidar nasarar da ta miƙa wa Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP.

Alkalan kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan-Osadebay, sun soke kuri’un ne bisa hujjar cewa babuda sitamfin INEC a jikinsu, wanda hakan ya saba wa dokar zabe, don haka ba halastattun kuri’u ba ne.

Hakazalika a zaman kotun na ranar Laraba, ta amince da dukkan bukatun da APC ta yi mata na cewa Abba ba halastaccen dan jam’iyyar NNPP ba ne, an saba wa dokar zabe ta 2022 sannan an yi amfani da kuri’un bogi a zaben.

Tuni dai jam’iyyar NNPP ta yi fatali da sakamakon sannan ta sha alwashin ɗaukaka kara.

A farko dai INEC ta sanar cewa Abba ya lashe zaben ne da ratar kuri’u 128,900, inda ya samu jimillar kuri’u 1,019,602, inda Nasiru Gawuna ya samu kuri’u 890,705.