Mutane da dama na fuskantar matsaloli iri-iri tun daga zamanai da suka wuce har ya zuwa kan namu.
Wasu za ka ga mutane ne ke quntata musu a wurare daban-daban, amma a yau ina so ka gane cewa kai ba saniyar ware ba ne domin ba a kan ka a fara ba, yesu da kansa ya samu kansa a irin wannan lamari kuma ya yi nasara babba, don haka muddin muna so mu samu nasara a kan irin duk wani hali da muka samu kanmu ciki, to sai mu bi irin hanyoyin da yesu da sauran almajiransa da manzannai suka bi, inda suka gane cewa nasarar da suka samu ta dalilin wahalhalun da suka sha ne da kuma Allah da ke tare da su wanda shi ya amince da haka.
To yawanci a yanzu matsalolin da muke fuskanta sun fito ne daga ’yan uwanmu mutane, inda idan wani ya yi maka wani abu, sai ka ji mutum ya ce har wane da na amince da shi ne ya yi mini haka? Ko kuma ka ji ya ce wannan da nake ganin najikina ne ko abokina shi ke da qarfin halin yi muni wannan abu?.
To ina so mudubi yadda yesu ya yi ga irin wadannan mutane da suka taso masa da kuma irin matakan daya dauka wanda har ya kaishi ga samun nasara.
Matakin farko da yesu ya dauka shi ne anfani da basirar da Allah ya bashi ta wajen fahintar mutane da kuma sanin a bin daya kamata yayi dominsu.
Idan akace ka fahinci mutum to zaka iya zama tare da shi haka kuma zaka iya hurda tare da shi, sau da yawa za ka ji ana fadin cewa wane mugu ne bayasan ganin kowa akusa da shi amma idan ka bincika da kyau sai kagane cewa duk da irin halin nan nasa yana da wani wadda yake jin dadin hurda da shi kuma suna da kyakkyawar fahimta da junansu.
Haka ma za ka ga mahaukaci na buge-buge ko doke-doke kowa kuma na gudunsa, amma da zarar yaga wani wanda yasan yadda yake bida shi sai kaga yabari.
Amma wani abu garayuwa irin ta ruhaniya sai ta banbanta da ta duniya.
Maganar Allah tace muyi addu’a domin magabtanmu wato wadanda suke gaba da mu. To sau da yawa zaka ga wannan batu na bai wa wasu mamaki suna cewa yaya za’a ce nayi wa wanda ke gaba dani addu’a? sai su manta cewa duk wanda ya saka mugunta da alheri ba karamar nasara yake samu ba.
A maimakon haka sai kaga sunfi maida hankali ga abin da ya faru dasu, ba za su iya tuna da cewa Allah ne ya qaddara hakan ba.
A rubuce yake cewa “yasan duka mutane don yariga yasan abin dake tare da mutum, shi yasa aduk lokacin da aka buqace shi daya yi wani abu wanda lokacin daya kamata yayi abin bai yiba, sai yace lokacinSa bai yi ba.
Haka kuma bai razana ba a daidai lokacin da yahuza iska riyoti ya bashe shi don ya riga yasan da cewa hakan zata faru idan har lokacin yayi.
Haka kuma a wasu lokuta yakan gayawa al’majiransa musamman manzanne guda goma sha biyun nan, inda yake cewa daya daga cikinku mayaudari ne.
“Ana nan tun kafin idin qetarewa, da yesu yasan lokacinsa yayi da zai ta shi daga wannan duniya ya koma wurin uba, da yake ya qaunaci mutanensa dake duniya ya qaunacesu har matuka” (yahaya, 13bs1) bama yasan za’a bashe shi kawai ba, harma da sanin wanda zai bashe shi da kuma lokacin da wannan abu zai faru.
Basirar da yake da ita wadda ta samo asali tun daga sama ita ce babbar mataqalar da ya hau har ta kai shi ga kariya daga cikin irin rayuwar da ake gudanarwa a cikin duniya da kuma sanin yadda zai bida ko wane lamari idan yataso.
Amma da ranar da za’a ba she shi ta zo, yasan cewa lokaci yayi da zai koma ga Uba a sama.
Don haka sai ya maida duk wasu abubuwa da ake yi masa a zaman cewa matakaine na ganin an cike duk wasu dalilan da suka sanya shi zuwa cikin duniya, harma ya fadi wata kalma da ke cewa “dan mutum zai koma kamar yadda yake a rubuce, don kuma kalmarnan da Annabawa suka fadi ya cika”.
Don haka yana da kyau ka kalli duk wani abin da kake fuskanta a zaman wani abune da Allah ya shirya a rayuwar ka don ka sami nasara idan ka kiyaye tare da juriya.
Irin wannan abu ne ya faru da Yakubu inda dan uwansa Isuwa ya dinga farautarsa don ya kashe shi, amma da ga bisani sai Yakubu ya gane cewa tsananin da yake fuskanta daga wajen dan uwansa da ke niyar kashe shi, wani abu ne wanda Allah ya shirya don ya faru a rayuwarsa wanda hakan yayi sanadiyar arziqinsa.
“yakubu yace “A’a ina roqon ka, indai na sami tagomashi a idonka, to sai kakarbi kyautar dake hannuna, gama haqiqa ganin fuskar ka, kamar ganin fuskar Allah ne, bisa ga yadda ka karbeni.
Ina kuma roqonka ka karbi kyautar dana kawo maka, gama Allah ya yi muni alheri matuqa, gama ina da abin daya ishe ni.
Da haka yakubu ya i masa, isuwa kuwa ya karba.
A yau mafi yawanmu da ke iqirari da sunan mabiya Almasihu muna fuskantar rauni musamman a duk lokacin da wata matsala ta taso ta rashin jin dadi ko kwanciyar hankali a tsakanin yan uwa na jinni ko kuma wadanda muke tare.
Raunin da muke fuskanta kuwa sun hada da rashin haquri, dauriya, da kuma bijirewa maganar Allah wadda a sakamakon hakan al’amura suka gaza daidaituwa.
An kai matsayin da za ka ga kirista ya tube riga yana fada a tsakanin al’umma, yayin da wani kuma ya maida zagi tamkar abincin yini wani kuma zamba ko cin rashawa da makamantansu ne ya sanya a gaba.
Irin wadannan mutane sukan fuskanci matsala ko kuma damuwa ne a sakamakon irin halin da suka sanya kansu ciki wadda suka sabawa dokokin Almasihu, don haka samun nasararsu a kan magabta zai kasance abu mai wuya.
Kadan daga cikin hanyoyin da ake son mabiyin Almasihu ya bi domin samun nasara a tsakanin magabta.