Hukumar NAPTIP mai yaki da safarar bil’adama a Najeriya ta ceto wasu mutum goma da aka yi fataucinsu a Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin kasar.
Reshen Hukumar NAPTIP na Arewa maso Yamma ne ya samu nasarar ceto mutanen da ke kan hanyar zuwa Jamhuriyyar Nijar domin yin aikatau.
- Buhari ya yi alhinin rasuwar Sarkin Kwatarkwashi
- Harin Coci: An soke bikin Ranar Dimokuradiyya a Ondo
Babban jami’in NAPTIP a shiyyar Arewa maso Yamma, Barista Abdullahi Babale, ya ce an ceto mutane ne wadanda aka yi fataucinsu daga Jihohin Kogi, Delta, Kwara, Oyo, Ondo, Legas, Ogun da kuma Osun.
Babale ya ce hukumar tare da hadin gwiwar rundunar hadin gwiwa da ke kula da shige-da-fice a kan iyaka, sun ceto mutanen wadanda suka kunshi maza biyu da mata takwas ’yan tsakanin shekaru 9 zuwa 28.
Ya ce, a halin yanzu ana ci gaba da ba su shawarwari a wani matsuguni da hukumar ta tanada, yayin da ake kokarin mika su ga ’yan uwansu.
Aminiya ta ruwaito cewa a watan Maris din da ya gabata ne Hukumar NAPTIP shiyyar Arewa maso Yamma ta yi nasarar ceto wasu mutum 35 da aka yi fataucinsu a Jihar Katsina.
NAPTIP ta ceto mutanen ne a iyakar Kwangwalam da ke Karamar Hukumar Mai Adua a kan hanyarsu ta tsallakawa Turai.