Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayar da tabbacin cewa ba za caji al’ummar Arewacin Nijeriya kudin wuta na tsawon lokacin da wutar yankin ta lalace ba.
Ministan ya sanar da haka ne a lokacin da yake bayar da tabbacin cewa nan da kwana biyar masu zuwa za a dawo da wutar da ta ɗauke a jihohi 17 da ke Arewacin Nijeriya.
Da yake jawabi bayan ganawa da Shugaba Tinubu, ministan ya ce zai tattauna da Hukumar Wutar Lantarki da daukacin Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki domin tabbatar da cewa ba a caji al’ummar kudin wutar da ba su sha ba.
Kimanin kwana 10 ke nan babu wuta a jihohi 17 na Arewacin Nijeriya sakamakon lalacewar babban layin lantarkin Shiroro zuwa Kaduna, wanda shi ke isar da wutar ga mafi yawan yankin Arewa.
Adelabu ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Tinubu ya umarci Shugaba Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa da Ofishin Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an gyara wutar.
Sannan ya ba wa al’ummar Arewa hakuri tare da cewa kamfanin wutar lantarki na ƙasa da hukumomin tsaro suna yin duk mai yiwuwa domin gyara wutar.
Ya kuma sanar cewa Majalisar Zartaswa ta Kasa ta amince a kara karfin babban layin lantarki na Shiroro-Kaduna wanda shi ne mafi tsufa a Nijeriya.
A cewarsa, idan aka kammala aikin, za a samu tsayayyiyar wutar lantarki a yankin Arewa.