Najeriya za ta yi amfani da tanade-tadaden doka wajen fara karbar haraji daga ribar da manyan kamfanonin sadarwa da ba a kasar suke ba amma suke da abokan hulda da yawa a cikinta.
Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da wakilan Kungiyar Akantoci ta Najeriya wacce shugabanta, Adesina Adebayo ya jagoranta zuwa Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
- ’Yan bindiga sun harbe mai juna biyu sun sace mijinta
- Ganduje zai biya wa dalibai 10,000 kudin jarrabawar NECO
Kakakin Mataimakin Shugaban Kasar, Laolu Akande a cikin wata sanarwa ranar Lahadi ya ambato Osinbajo na cewa, “Duk da yake Gwamnatin Tarayya ba za ta kara haraji a yanzu ba, amma Dokar Kudi ta 2019 ta bata damar fadada hanyoyin samun kudin shiga.
“Wannan ya kunshi karbar harajin daga manyan kamfanonin sadarwa na duniya da suke da tarin abokan hulda a Najeriya, ko da kuwa basu da matsuguni na dindindin a nan kuma yanzu haka ba sa biyan harajin.
“A kan haka, sashe na hudu na Dokar Kudi ta 2019, ta ba Ministar Kudi karkashin izinin Shugaban Kasa, damar tantance me ake nufi da samun abokan hulda da yawa ga kamfanonin da ba na Najeriya ba.
“Mun fuskanci matsananciyar koma baya ta fuskar tattalin arziki wanda hakan yake nufin ba zai yiwu mu matsa da karbar haraji ba saboda mutane a fusace suke.
“Ina jin abu mafi muhimmanci yanzu shine mu fadada hanyoyin karbar haraji domin wadanda basa biya su fara biya.
“Na tabbatar kuna da masaniya a kan irin wadannan shirye-shiryen, ciki har da tsarin bayyana kadarori (VAIDS), wanda wani yunkuri ne na kara masu biyan harajin, ciki har da masu kadarori a kasashen waje,” inji Osinbajo. (NAN).