Sarkin Kano na 14, Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu, ya bayyana cewa Najeriya a yanzu tana cikin wani mawuyacin hali fiye da yadda da ta tabarbare a shekarar 2015.
Sarki Sanusi ya bayyana damuwa kan halin da Najeriya ke ciki, yana mai cewa, kasar ta tabarbare fiye da yadda take a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki daga hannun Goodluck Jonathan.
- Rarara ya raba tallafin kudi ga ’yan Kannywood
- Sarkin Bichi ya shirya taron addu’o’i saboda matsalar tsaro
Tsohon Gwamnan Babban Bankin kasar ya bayyana hakan ne a wurin wani taro da Gidauniyar Akinjide Adeosun ta shirya kan sha’anin shugabanci a Jihar Legas.
“Wannan ita kadai ce kasar da ke samar da man fetur amma take kokawa a halin yanzu duk da cewa farashin man ya tashi sanadiyyar rikicin Rasha da Ukraine.
“A yanzu duk kudaden shigarmu ba za su iya biyan basussukanmu ba. Wannan ya nuna muna cikin musiba.
“Kuma gaskiyar magana ita ce, akwai ‘yan Najeriya da dama, wadanda idan aka ba su dama za su inganta al’amura a kasar amma ba su da halin fitowa takara a irin wannan yanayi da ake ciki.
Ya kuma yi gargadin cewa, abin da aka gani a 2015 nafila ne kan abin da zai faru a 2023, yana mai cewa, a halin yanzu Najeriya na fama da matsaloli da dama da suka hada da ta’addanci, hare-haren ‘yan bindiga da tsadar rayuwa da rashin tabbas kan farashin kudaden ketare.
Sanusi ya kuma diga ayar tambaya yana mai cewa, ta yaya tarihi zai tuna shugaban kasa da gwamnoni da ministoci da suka shafe tsawon shekaru takwas kan karagar mulki?
Ya danganta kalubalen da Najeriya take fuskanta a yanzu da rashin hangen nesa na wasu shugabanni a kasar.
“Mafi akasarin masu rike da mukamai a Najeriya na da hangen nesan da ya takaita ne kadai ga zabe mai zuwa domin su ci nasara,” inji shi.