Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da harin da Isra’ila ta kai sansanin fararen hula a Rafa, inda ta yi kira da a yi ƙoƙarin maido da zaman lafiya a yankin.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Ministan Harkokin Wajen Ƙasar, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce: “Gwamnati da al’ummar Najeriya sun yi Allah wadai a cikin kakkausar murya game da harin da aka kai kan fararen hula da ba su da kariya a halin yanzu a Gaza a ci gaba da rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa.’
Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kudancin Gaza a ranar Lahadi 26 ga watan Mayu ya kashe mutum aƙalla 45, mafi yawan su mata da ƙananan yara, lamarin da ya ƙara yawan hare-haren da aka kai kan fararen hula tun bayan ɓarkewar yaƙin.
Ministan ya koka da yadda aka riƙa samun rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da cin zarafin ɗan Adam da kuma hana shigar da kayan tallafi Gaza.
Najeriya ta buƙaci a gaggauta komawa tsarin kiyaye ’yancin ɗan Adam, musamman hana kisan gilla da kuma kare fararen hula da ke Gaza daga duk wani harin soji.
Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da Isra’ila da Hamas da kuma Majalisar Dinkin Duniya su ƙara mayar da hankali wajen kawo ƙarshen rikicin Gaza domin tsagaita wuta da kuma ceton fararen hula a yankin.
“Saboda haka Najeriya ta damu matuƙa game da tsaro da jin daɗin fararen hula na Gaza kamar yadda ta shafi kare martaba da tsarin rayuwar ɗan Adam a yankin.”
Ƙasar ta yi Allah-wadai da harin da jin ƙai da ya taso daga halin da ake ciki.