Najeriya ta katse wutar lantarkin da take ba wa makwabciyarta Jamhuriyar Nijar a wani mataki na karin matsin lamba ga sojojin kasar da suka yi wa Shugaba Mohamed Baozum juyin mulki.
Katse wutar da Najeriya ta yi ta jefa Yamai, babban birnin Nijar, kasar da ta fi dogaro da ita wajen samun wutar lantarki a cikin duhu.
- Yanzu-yanzu: Masu Zanga-Zangar cire tallafin mai Sun Ɓalle Ƙofar Majalisa
- Yanzu-yanzu: Hafsoshin Tsaron ECOWAS na taro kan juyin mulkin Nijar
Hakazakila matsalar ta addabi manyan birane irin su Maradi da Zindar a kasar Nijar wadda a baya ba ta san da daukewar wuta ba kamar Najeriya.
Lamarin ya kai ga kamfanin wutar lantarki na Nijar ya koma ba wa yankunan kasar wutar na wani lokaci sannan ya mayar wa wadanda ba su samu ba daga baya, a bisa tsarin karba-karba.
Kamfanin ya dora matsalar kan katse musu wuta daga Najeriya, wanda hakan ya sa aka koma ba wa wasu wuraren wuta na kimanin sa’a guda, sannan a dauke na kimanin sa’o’i biyar kafin a sake dawo musu da ita.
A halin yanzu dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ne ke jagorantar kungiyar raya tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS), wadda ta kakaba wa sabuwar gwamnatin sojin Nijar takunkumai ciki har da na tattalin arziki.
ECOWAS da manyan kasashen duniya kawayen Nijar sun yi barazanar daukar matakan soji a kan sabuwar gwamnatin sojin, muddin ba ta mika wa Mista Bazoum mulkinsa da ta kwace ba.
Najeriya ta yanke wa Nijar wutar ne a matsayin wani bangare na takunkuman da kungiyar ta kakaba wa sabuwar gwamnatin sojin ta Nijar.
Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da hukumance daga gwamnatin Najeriya dangane da hakan, ko da yake kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito wasu majiyoyin gwamnati sun tabbatar da katse layukan da ke kai wa Nijar wuta.
Daukar mataki kan Nijar
A ranar Laraba ne dai manyan hafsoshin tsaron kasashen ECOWAS suka fara wani taro a Najeriya kan juyin mulkin na Nijar.
Manyan hafsoshin tsaron Nijar makwabtan Nijar – Mali, Guinea Bissau, Burkina Faso – da ke hannun sojojin da suka yi juyin mulki sun kaurace wa taron.
Gwamnatocin sojojin kasashen uku dai sun yi barazanar yakar dakarun ECOWAS ko duk wata kasa da ta yi kokarin yi wa sabuwar gwamnatin sojin Nijar shisshigi.
Rundunar tsaron fadar shugaban kasar Nijar ne suka kifar da gwamnatin Bazoum, suka kuma nada kwamandansu, karkashin kwamandanta, Janar Abdourahmane Tchiani a masayin shugaban kasa na mulkin soji.
Sojojin sun jingine kundin sarin mulkin are da ure iakokin kasar, amma a ranar alaa sun sanar da bude iyakokin kasar da kasashen Chadi, Burkina Faso, Mali, Libya da kuma Algeriya.