Bankin Duniya ya ce Najeriya ta shiga cikin jerin kasashe 10 mafiya fuskantar kantar bashi a duniya.
Bankin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar a makon nan kan yanayi basussuka da ci gaba da ake samu.
- Kasafin Shekara Guda Ba Zai Biya Bashin Da A ke Bin Najeriya Ba
- An yi garkuwa da yaro mai wata 8 a Zamfara
Alkaluman sun bayyana cewa, Najeriya ta kasance ta biyar a jerin kasashen da bashi yafi yi wa katutu inda basussukan da ake bin ta ya kai $11.7bn kimanin Naira Tiriliyan 4.8.
Kasar Indiya ce a sahun gaba inda ake bin ta $22bn, sai Bangladesh $18.1bn.
Akwai Pakistan ita ma da basussukanta suka kai $16.4bn, sai Vietnam $14.1bn.
Sauran kasashen da ke cikin wannan jerin 10, akwai Habasha wato Ethiopia mai $11.2bn.
Kenya ta ciyo bashin $10.2bn, Tanzania $8.3bn, Ghana ta na da $5.6bn, sai kuma Uganda mai $4.4bn.
Sanarwa ta kuma kara da cewa kudaden da Bankin Duniya kadai ke bin Najeriya wanda ba a raba ba sun kai $8.656bn ya zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2021.