Najeriya ta samu kyautar na’urar da ke iya fitar da sakamako fiye da dubu uku na gwajin cutar coronavirus a rana guda.
Gwamantin Birtaniya ta ba wa Najeriya kyautar na’urar mai sana ‘Polymerase Chain Reaction’ (PCR a takaice), ta kuma mika ta ga Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) a Legas inda cutar ta fi kamari a Najeriya.
Sanarwar da Ofishin Mataimakin Jakadan Birtaniya a Najeriya ya fitar ta ce PCR ita ce na’ura mafi sahihanci wajen gano cutar coronavirus kuma tallafin na daga cikin hadin gwiwar kasashen biyu domin dakile yaduwar cutar a Najeriya.
Kakakin ofishin, Ndiamaka Eze, ta ce gwamnatin Birtaniya ta saya wa Najeriya PCR din ne daga asusun tallafin UKAid.
- Najeriya ta karbi tallafin kayan yakar coronavirus na Dala miliyan 22
- Yadda za a rage mace-macen COVID-19 a Najeriya
“Birtaniya na aiki tare da hukumomin Najeriya ciki har da NCDC domin tallafa wa shirye-shirye da tsare-tsaren hana yaduwar cutar a Najeiya”, inji ofishin jakadancin.
Da yake karbar kayan, Darekta Janar na NCDC, Chikwe Ihekweazu, ya ce, “Muna farin cikin samun wannan gagarumin tallafi daga Hukumar DFID na gwamnatin Birtaniya.
“Sabuwar PCR din…za ta taimaka wajen cimma manufarmu ta yi wa fiye da mutum miliyan biyu gwajin cutar coronavirus a nan da watanni uku masu zuwa”, inji shi.