Najeriya ta koma ta 31 a jerin kasashe mafi kwarewa a kwallon kafa da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya fitar.
Hakan na zuwa duk da tawagar ta Super Eagles ta lallasa Sao Tome and Principe da ci 10-0, a wasan share fage na gasar cin Kofin Afirka.
- Yadda namiji ya rika amfani da sunan mace yana damfarar maza a Facebook
- Kotun Koli ta yi fatali da bukatar Buhari ta sauya Dokar Zabe
Sai dai Super Eagles wadda ta nada sabon koci, Jose Peseiro ta ci gaba da zama ta hudu a Afirka.
Najeriya ta fara wannan shekarar ne a ta 32, inda ta samu ci gaba bayan da ta dawo na 30 a watan Maris, kafin ta kara sauka zuwa ta 31 a jadawalin na FIFA.
Senegal wadda ita ce ta daya a Afrika ta dawo ta 18 a teburin duniya, daga ta 22 a watan Maris.
Sai dai Brazil ta kara bai wa Belgium rata a matsayin ta daya, yayin da Argentina ta sauko da Faransa daga ta uku.