Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunci kan masu cin zarafin mata a ko’ina su ke a Najeriya don zama izina ga na baya.
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan a Abuja a yayin taron gangami da kaddamar da wasu cibioyi na musamman don yaki da matsalar, mai suna “Spotlight initiative” da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Tarayyan Turai suka taimaka wajen kafawa.
Ministan ya ce aikin wanda zai hada hukunta masu cin zarafin mata a makarantu da wuraren aiki da sauransu, ya samu goyon bayan gwamnoni ta kunqiyarsu ta kasa.
A jawaban da suka gabatar, babban jami’in MDD a Najeriya Mattias Schmale da wakilyar Tarayyar Turai da kuma ECOWAS Samuela Isopi sun ce shirin na samun nasara inda mata da aka ci zarafinsu ke kai korafi zuwa ofishin tare da tabbatar da ganin an tallafa musu waen farfado da rayuwarsu da aka tagayyara.
- CBN zai rufe asusun bankin marasa BVN
- Rabin mutanen Arewa maso Gabas na da matsalar kwakwalwa —Masana
Sun ce an mika cibioyin ga gwamnati kai-tsaye wanda da ma da hadin gwiwarta aka kafa su, don ci gaba da gudanar da su kai-tsaye.
“Ministan tattalin arziki qasa sanata Atiku Bagudu wanda Dr. Lanre Akanye ya wakilta ya ce an samu nasarar sosai a shirin tun lokacin da ya faro a shekara ta 2018 wajen tallafawa matan da a ka ci zarafi don farfado da rayuwarsu.
Sanata Atiku Bagudu ya yaba bisa tallafin kasashen Tarayyan Turai da ke ware kashi 5 cikin 100 na kasafinsu, inda Najeriya ke amfana da wajen miliyan 500.
Daya daga cikin iyayen al’umma da suka halarci taron, Sarkin Shonga Dokta Halliru Yahaya ya ce ci gaba da cin zarafin mata na iya yin illa wajen raunana neman ilimi na ‘ya mace da kuma gudanar da aiki da ke buqantan jinsinsu, inda ya buqaci al’umma da su baiwa shirin goyon baya ta hanyan fallasa masu aikata laifukan don hukunta su