Hukumar Tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano, ta soke lasisin gidajen wasannin gala guda takwas bisa karya wasu dokokinta.
Idan za a tuna a kwanakin baya hukumar, ta soke lasisin wasu gidajen galar bisa samun su da laifin karya dokar hukumar.
- Ma’aikatan wutar lantarki sun tsunduma yajin aiki a Kano
- Sojoji da ’yan siyasa na taimaka wa Boko Haram da bayanai — Zulum
Cikin sanarwar da kakakin hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ya zayyano wuraren da hakan ta shafa da suka haɗa da Hamdala Entertainment, Lady J Entertainment, Ɗan Hausa Entertainment da Ni’ima.
Sauran sun haɗa da Babangida Entertainment, Harsashi Entertainment, da kuma Wazobiya.
Idan ba a manta ba hukumar a baya-bayan nan ta dakatar da haska wasu fina-finai 22 da suka haɗa da Dadin Kowa, Labarina, Garwashi, Gidan Sarauta da wasu.
Amma bayan wani taron masu ruwa da tsaki na Kannywood an bai wa masu shirya fina-finan wa’adin mako guda don tantance su.
A ranar Talata ma hukumar ta dakatar da yin tallan magungunan gargajiya a cikin fina-finai ko a kan titin har sai an tantance su.