✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano za ta hukunta masu shigar banza a bikin Sallah

Yunkuri ne na gwamnatin domin tsaftace yadda gidajen wasanni da kidan DJ ke shagalin bikin Sallah.

Gwamnatin Kano ta sha alwashin hukunta masu shigar banza ko cudanya maza da mata a lokacin bukukuwan Sallah Karama da za a yi.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Dab’i ta Kano, Abba Almustapha a wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, inda ta ce matakin yunkuri ne na gwamnatin domin tsaftace yadda gidajen wasanni da kidan DJ ke shagalin bikin Sallah.

“A kokarin ta na yaki da rashin da’a tare tsaftace yadda gidajen wasanni da masu kidan DJ za su gudanar da shagalin bikin sallah a Kano, Hukumar tace fina-finai da Dab’i karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta bayyana shirinta na saka kafar wando daya da duk wani gidan wasa ko mai kidan DJ da aka samu da rashin da’a a yayin gudanar da bikin sallah a Jihar.

Hukumar ta shirya wata tawaga ta musamman da za ta kewaya gidajen wasannin a bikin sallah karkashin kulawar Alh. Abubakar Zakari Garun Babba Daraktan Dab’i na Hukumar, domin sanya ido da tabbatar ba a bai wa masu shigar banza ko shaye – shaye damar shiga gidajen wasannin ba.

“Haka kuma, hukumar ta hana hada maza da mata a guri daya a yayin bikin sallar. Tawagar za ta yi aiki ne dare da rana daga ranar daya ga sallah har zuwa lokacin da za’a kammala bikin sallar domin cimma nasarar aikin da ta sanya a gaba.”

El-mustapha ya kuma yi gargadi ga masu gidajen wasanni da masu sana’ar DJ, da su yi biyayya ga dokokin hukumar sau da kafa domin gujewa fushinta.